Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja
- Gwarazan yan sanda a jihar Neja sun hallaka yan bindiga akalla 10 a wani gumurzu da suka yi
- An fafata tsakanin yan sandan da maharan, inda suka samu nasarar fatattakar su daga kai hari ƙauyen Kundu
- Gwamnan jihar, Abubakar Bello, ya yabawa jami'an, sannan yayi ta'aziyya gare su bisa rasa mutum biyu
Aƙalla yan bindiga 10 aka hallaka yayin da jami'an yan sanda a jihar Neja suka daƙile wani harin yan bindiga ƙauyen Kundu, ƙaramar hukumar Rafi ranar Lahaɗi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Jagoran Yan Bindiga, Turji, Ya Sako Daruruwan Mutanen da Ya Sace a Zamfara
A cewar wani mazaunin ƙauyen, jami'an yan sanda biyu sun rasa rayuwarsu yayin artabu da maharan, kamar yadda punch ta ruwaito.
Gwamna yakai ziyara yankin
Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya ziyarci yankin da lamarin ya faru domin yin ta'aziyya ga jami'an yan sanda da kuma yaba musu bisa wannan sadukarwa.
Bello ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na tsamo jihar daga matsalar tsaron da take ciki.
A jawabinsa, Gwamnan yace: "Ina mai taya ku murna bisa wannan nasara, ina mai tabbatar muku da cewa duk abinda kuke buƙata domin sauke nauyin dake kanku, zamu samar da shi."
"Ina fatan zaku bamu haɗin kai kuma ina tabbatar muku zamu yi iyakar karfin mu wajen ganin kun samu duk kayan aikin da kuke buƙata."
KARANTA ANAN: Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura
Mun gama shirin samar da kayan aiki
Gwamna ya ƙara da cewa gwamnatin Neja ta kammala duk wasu shirye-shirye na samar wa jami'an tsaro da kayan aiki domin magance matsalar tsaro.
Ya bayyana cewa ba da jimawa ba kayan aikin zasu ƙariso kuma za'a damka muku su don cigaba da aikin ku.
A wani labarin kuma Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, ya amince da korar Sabo Muhammad Ahmad, shugaban makarantar sakandiren gwamnati dake Ɗanbatta (GSS) saboda saɓawa dokar hutun sallah (eid-el-kabir).
An kori shugaban makarantar ne bayan ya gaza riƙe ɗalibai 300 dake rubuta jarabawar kammala sakandire NECO a makarantarsa duk da umarnin hana ɗaliban tafiya hutun sallah da aka ba shi.
Asali: Legit.ng