Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura
- Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, yace ba yadda za'ai Najeriya ta canza zuwa tura sakamakon zaɓe ta Na'ura kai tsaye
- Hukumar NCC tace kashi 50% na sassan Najeriya kacal zasu iya aika saƙon sakamako ta na'ura ba tare da matsala ba
- Sanatan yace babu yadda za'ai ace rabin yan Najeriya ne kaɗai za'a ƙidaya kuri'unsu
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bayyana dalilin da yasa majalisar ta tafka muhara kan dokar tura sakamakon zaɓe ta na'ura, kamar yadda leadership ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah
A ranar Alhamis da ta gabata ne sanatoci suka cimma matsaya cewa "Kafin INEC ta aiwatar da tura sakamakon zaɓe ta na'ura sai hukumar NCC ta tabbatar da ingantaccen sabis na yanar gizo kuma yan majalisa sun amince."
Lawan ya bayyana cewa majalisar da yake jagoranta ta cimma wannan matsaya ne domin kare muradun sama da rabin yan Najeriya, waɗanda ba za'a ƙirga ƙuri'un su ba idan aka aiwatar da dokar kai tsaye.
Shugaban sanatocin ya faɗi haka ne yayin fira da yan jarida lokacin da yakai ziyara mazaɓarsa Yobe ta arewa a jihar Yobe, kamar yadda punch ta ruwaito.
Majalisa ta amince da gyaran kundin dokokin zaɓe
Da yake jawabi dangane da amincewa da dokokin zaɓe da aka yiwa garambawul, Sanata Lawan, yace:
"Nayi farin ciki mun amince da gyaran dokokin zaɓe duk da wasu na ƙorafin matsayar da muka cimma wa da kuma wadda majalisar wakilai ta amince da ita."
"Yayin da mafi yawan sanatoci suka zaɓi rashin amincewa da dokar tura sakamakom zaɓe daga runfar zaɓe zuwa gunduma zuwa ƙaramar hukuma zuwa jiha har zuwa ƙasa, ba suna nufin basu yarda da dokar bane."
"Gaba ɗaya mun amince ya kamata mu canza tsarin zaɓen mu ta yadda za'a samu sauki wajen tura sakamako da kuma sahihancin zaɓen."
Bamu da isasshen sabis a faɗin ƙasa
Sanatan ya ƙara da cewa:
"Amma kuna gani, bamu kai wannan matsayin ba da zamu canza lokaci guda zuwa tura sakamako ta na'ura a kowane ɓangare a Najeiya, saboda haka dole mu kula."
Ba zai yuwu ace aƙalla kashi 50% na yan Najeriya ba zasu yi zaɓe ba, ko kuma ba za'a ƙidaya ƙuri'unsu ba kuma kace wai ba wani abu bane, mu fara aiwatar da dokar nan take."
"Hukumar sadarwa (NCC) ta bayyana cewa kashi 50% na runfunan zaɓe a Najeriya ne zasu iya aika sakamakon zaɓe ta na'ura domin sune suke da sabis."
KARANTA ANAN: Da Duminsa: IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi
Ba sanatocin APC ne kaɗai ba
Shugaban sanatocin ya musanta rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka buga cewa sanatocin APC ne kaɗai suka yi fatali da dokar.
"Ba wai yan APC ne kaɗai ba, akwai sanatocin PDP da basu amince da aiwatar da dokar kai tsaye ba, amma naga wasu kafafe na watsa cewa yan APC ne kaɗai," inji shi.
A wani labarin kuma Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun
Mutum 14 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Ipetu Ijesa, jihar Osun, da yammacin Asabar.
Kwamandan jami'an hukumar FRSC na jihar, Paul Okpe, ya bayyana cewa tseren wuce wani ne ya haddasa hatsarin.
Asali: Legit.ng