Da Duminsa: IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi

Da Duminsa: IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi

  • IGP Usman Baba, ya umarci kwamishinonin yan sanda dake faɗin ƙasar nan su tabbatar an yi shagulgulan sallah lafiya
  • Wannan na zuwa ne yayin da musulmai ke gab da fara shagulgulan bikin babbar sallah (Eid-el-kabir)
  • Sufetan ya taya ɗaukacin al'ummar musulmin Najeriya barka da sallah, da fatan za'a yi sallah lafiya

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinonin yan sandan ƙasar nan da su ɗauki matakan tsaurara tsaro a wurraren ibada da manyan hanyoyi yayin da babbar sallah (Eid-el-kabir) take ƙaratowa, kamar yadɗa punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun

IGP ya faɗi hakane a wani jawabi mai taken, 'Bikin sallah: IGP ya bada tabbacin tsaro da aminci' wanda kakakin hukumar, Frank Mba, ya fitar ranar Lahadi.

Sufetan Yan sanda na ƙasa, IGP Usman Alkali Baba
Da Duminsa: IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

IGP ya taya musulmai murna

A cikin jawabin, IGP ya taya ɗaukacin al'ummar musulmai murnar zagayowar babbar sallah ta shekarar 2021, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah

Sufetam ya kuma jaddada ƙoƙarin yan sanda na cigaba da samun nasarori wajen kare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasa.

Haƙanan ya bayyana cewa jami'an yan sanda zasu cigaba da namijin ƙoƙarin da suke yi wajen daƙile duk wani harin ta'addanci da yan ta'adda a Najeriya.

A bi doka da kare yaɗuwar cutar COVID19

Shugaban yan sandan ya roƙi yan Najeriya da su yi murnar sallah cikin farin cikin kuma su cigaba da bin dokokin tsaro da na kare yaɗuwar cutar COVID19.

Wani sashin jawabin yace:

"Sufetan yan sanda ya na tabbatarwa yan ƙasa cewa hukumar zata ƙara a kan ƙoƙarin da take da yaƙi da ta'addanci da yan ta'adda, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

"IGP ya kuma umarci kwamishinonin yan sanda na jihohi da mataimakansu da su kara matakan tsaro yayin da babbar sallah take gabatowa."

KARANTA ANAN: Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

Kara karanta wannan

Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

"Sufetan ya umarce su da su ɗauki matakan da ya kamata domin tabbatar da an yi sallah an ƙare lami lafiya a faɗin ƙasar nan."

A wani labarin kuma Bayan Dambarwar Yan Majalisu, Hukumar INEC Ta Maida Martani Kan Tura Sakamako Ta Na'ura

Hukumar INEC, ta bayyana cewa ta na ƙarfin da zata iya aiwatar da tura sakamakon zaɓe ta na'ura.

Wannam na zuwa ne bayan cece-kucen da yan majalisu biyu suka yi a kan sabuwar dokar tura sakamako ta na'ura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel