Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah
- Gwamnatin Kano ta sallami shugaban makarantar sakandiren gwamnati dake Ɗanbatta
- Wannan hukucin ya biyo bayan bada hutun sallah da shugaban yayi ga ɗaliban ajin ƙarshe
- Gwamnatin Kano ta kudiri aniyar kyautata wa ɗaliban dake rubuta NECO yayin da zasu yi sallah a makarantunsu
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, ya amince da korar Sabo Muhammad Ahmad, shugaban makarantar sakandiren gwamnati dake Ɗanbatta (GSS) saboda saɓawa dokar hutun sallah (eid-el-kabir), kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Duminsa: IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi
An kori shugaban makarantar ne bayan ya gaza riƙe ɗalibai 300 dake rubuta jarabawar kammala sakandire NECO a makarantarsa duk da umarnin hana ɗaliban tafiya hutun sallah da aka ba shi.
Kiru ya ƙara da cewa Mr. Ahmad ya baiwa ɗaliban hutu kuma ya tsallake ya tafi mahaifarsa domin yin sallah a can ba tare da sanar da ma'aikatar ilimi ba.
Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura
"Wannan abun da yayi ya ya saɓa mana kuma ya ci amanar yardar da muka yi masa, sannan hakan saɓa wa doka ne." inji kwamishinan.
Kiru ya umarci Ahmad da ya kawo kansa ma'aikatan ilimi ranar Litinin domin cigaba da abinda ya kamata.
Ɗaliban dake rubuta NECO ba zasu je hutu ba
Idan zaku iya tunawa gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan makarantun sakandiren kwana da su riƙe ɗaliban dake rubuta jarabawar NECO.
Gwamnatin ta bayyana kudirinta na samar musu da abinci da ya kamata yayin bikin sallah wanda ya haɗa da siyo musu shanu 19.
KARANTA ANAN: Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta kammala duk shirye-shiryen da ya kamata domin kyautata wa ɗaliban su yi bikin salla a makarantunsu.
A wani labarin kuma Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto
Ambaliyar ruwa sanadiyyar ruwa mai ƙarfi ya laƙume rayukan yan mata biyu tare da dabbobi sama da 140.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ja'oje dake ƙaramar hukumar Wamakko, inda gidaje dama suka rushe.
Asali: Legit.ng