Da Dumi-Dumi: Jagoran Yan Bindiga, Turji, Ya Sako Daruruwan Mutanen da Ya Sace a Zamfara
- Yan bindiga sun sako mutanen da suka kama a ƙauyukan jihar Zamfara a ƙarshen makon nan
- Wannan ya biyo bayan kame mahaifin shugabansu Turji da jami'an tsaro suka yi a jihar Jigawa
- Rahoto ya bayyana cewa sai da aka saki mahaifinsa sannan ya sako mutanen da ya sace
Jagoran yan bindiga a jihar Zamfara, Turji, ya sako dukka mutanen ƙauyuka da matafiyan da mutanen sa suka sace a ƙarshen mako, domin ya jawo hankali bisa damƙe mahaifinsa da jami'an tsaro suka yi.
KARANTA ANAN: Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura
Dailytrust ta ruwaito cewa Turji ya yi awon gaba da ɗumbin mutane a Zamfara makonni biyu bayan an kame mahaifinsa a Kazaure, jihar Jigawa.
Rahoto ya bayyana cewa an maida mahaifin nasa jihar Jigawa bayan ya gaza hana ɗansa ayyukan ta'addancin da yake yi.
An kame shi ne bayan samun bayanan sirri daga wata tawagar dake adawa da turji, inda suka faɗa wa jami'an tsaro cewa mahaifin Turji yazo siyar da shanun da ɗansa ya sato.
A wasu jerin hare-hare kan ƙauyukan, Kware, Kurya, Badarawa, Keta da Maberaya, yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama tare da shanu.
An saki mahaifin Turji
Wata majiya ta shaidawa jaridar dailytrust cewa waɗanda suka shiga tsakani sun kaiwa Turji mahaifinsa ranar Lahadi da yamma.
Majiyar ta ƙara da cewa shugaban yan bindigan ya amince ya saki waɗanda ya kama a wani ɓangaren na tattaunawar sulhu da gwamnati ta ƙirƙiro don daƙile ayyuakn yan bindiga.
KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah
"Ya saki mutanen bisa ratsin kansa saboda waɗanda suka shiga tsakani sun nemi yayi hakan," wata majiyar jam'an tsaro ta faɗa.
A baya dai, ya bayyana cewa ba zai saki mutanen ba har sai jami'an tsaro sun sako masa mahaifinsa dake hannunsu.
A wani labarin kuma IGP Ya Bada Umarnin Tsaurara Tsaro a Manyan Hanyoyi da Masallatan Idi
IGP Usman Baba, ya umarci kwamishinonin yan sanda dake faɗin ƙasar nan su tabbatar an yi shagulgulan sallah lafiya.
Wannan na zuwa ne yayin da musulmai ke gab da fara shagulgulan bikin babbar sallah (Eid-el-kabir).
Asali: Legit.ng