Bayan Dambarwar Yan Majalisu, Hukumar INEC Ta Maida Martani Kan Tura Sakamako Ta Na'ura
- Hukumar INEC, ta bayyana cewa ta na ƙarfin da zata iya aiwatar da tura sakamakon zaɓe ta na'ura
- Wannam na zuwa ne bayan cece-kucen da yan majalisu biyu suka yi a kan sabuwar dokar tura sakamako ta na'ura
- INEC tace a baya ta amshi sakamakon zaɓe daga ƙauyukan dake nesa sosai da birane inda al'umma take
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta bayyana cewa zata iya tura sakamakon zaɓe ta na'ura daga kowane yanki a Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto
Punch ta rahoto cewa yan majalisun tarayya sun sha cece-kuce a kan tura sakamakon zaɓe ta na'ura, inda wasu suka nuna rashin amincewarsu da dokar.
Dambarwa ta ɓarke a majalisar wakilan tarayya ranar Alhamis, yayin da mambobin suka tafka muhara kan sashi na 15 (2) a dokokin zaɓe da aka yiwa garambawul, wanda yake ɗauke da tura sakamako ta na'ura.
Sanatocin APC sun ƙi amincewa
Hakazalika a majalisar dattijan Najeriya, sanatocin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) sun nuna rashin amincewarsu da dokar, inda aka kawo kudurin da zai tilastawa INEC neman izinin hukumar sadarwa NCC da kuma yan majalisu kafin ta fara aiwatar da dokar.
A cewar wasu sanatocin da suka yi fatali da dokar, wasu sassan ƙasar nan babu isasshen sabis ɗin da za'a tura sakamakon.
Hakanan wani kwamishinan NCC, ya bayyana wa mambobin majalisar wakilai cewa kashi 50% na ƙasar nan kacal ne yake da sabis ɗin 3G.
Zamu iya tura sakamako ta na'ura
Amma da yake fira da gidan talabishin na channels tv, Kwamishinan yaɗa labarai da rijistar zaɓe na INEC, Festus Okoye, ya nuna cewa matsayar hukumar zaɓe a bayyane take.
KARANTA ANAN: Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kuɓutar da Wani Yaro da AkaɓSace a Cikin Akwatin Gawa
Yace: "Mun tura sakamakon zaɓe daga yankin da suke nesa da al'umma, har ma da yankunan da sai anyi amfani da yan dako."
"Saboda haka matsayar INEC a bayyane take cewa muna da ƙarfi da ikon yin amfani da fasahar zamani a yyukan zaɓe."
"Amma duk wani aikin mu, muna yin shi ne cikin doka, kuma zamu cigbaa da kasancewa cikin biyayya ga kundin dokar zaɓe."
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan
Yan bindiga sun sake kai hari garin Igangan da daren ranar Jumu'a, inda suka hallaka mutane da dama.
Rahoto ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka kashe a harin harda wani kwamandan jami'an tsaron Amotekun.
Asali: Legit.ng