Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun

Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun

  • Wani mummunan hatsari ya hallaka mutum aƙalla 14 a yankin Ipetu Ijesa dake jihar Osun
  • Kwamandan jami'an hukumar FRSC na jihar, Paul Okpe, ya bayyana cewa tseren wuce wani ne ya haddasa hatsarin
  • Jami'an FRSC sun kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawa dake asibiti mafi kusa

Mutum 14 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Ipetu Ijesa, jihar Osun, da yammacin Asabar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

Premium times ta rahoto cewa, hatsarin ya rutsa da wata motar Sienna mai lambar rijista KRD 842 KY da kuma babbar motar kaya mai lamba BAU 171 KE.

Waɗanda hatsarin ya kashe sun haɗa da ƙananan yara mata biyu, ƙananan yara maza huɗu, samari huɗu da kuma yan mata huɗu.

Kara karanta wannan

Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

Hatsari ya hallaka mutum 14 a Osun
Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Yara da Matasa da Dama a Osun Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An kai waɗanda abun ya shafa Asibiti

Jami'an hukumar kare haɗurra ta ƙasa (FRSC) da suka isa wurin sun ƙai waɗanda suka ji raunuka asibiti, sannan sun kai gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa.

Kwamandan FRSC na jihar Osun, Ƙwamanda Paul Okpe, ya bayyana cewa ana tsammanin hatsarin ya auku ne sanadiyya tseren wuce juna.

Okpe wanda ya yi magana ta bakin kakakin hukumar FRSC ta jihar, Mrs Agness Ogungbemi, yace an kai gawarwakin zuwa ɗakin ajiye gawa.

KARANTA ANAN: Bayan Dambarwar Yan Majalisu, Hukumar INEC Ta Maida Martani Kan Tura Sakamako Ta Na'ura

Yace: "Jami'an mu sun isa wurin da misalin ƙarfe 5:50 ma yamma, inda suka tarad da gawarwakin waɗanda abun ya rutsa da su, daga nan muka ɗauke su zuwa asibiti mafi kusa, Asibitin Wesley a Ilesa."

A wani labarin kuma Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kuɓutar da Wani Yaro da Aka Sace a Cikin Akwatin Gawa

Kara karanta wannan

Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kubutar da Wani Yaro da Aka Sace a Cikin Akwatin Gawa

Jami'an tsaron hukumar shige da fice sun samu nasarar kuɓutar da wani yaro ɗan shekara 12 a cikin akwatin gawa.

Mutanen da suka yi ƙoƙarin sace yaron sun saka shi cikin akwatin gawa kuma sanye da fararen kaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262