Da Dumi-Dumi: Bayan Cece-Kuce, Sanatoci Sun Amince da Naɗin Wani Kwamishinan Zaɓe, INEC
- Bayan sun ƙi amincewa ranar Talata, Sanatoci sun amince da naɗin farfesa Adam a matsayin kwamishinan Zaɓe
- Wannan ya biyo bayan nazari da sanatocin suka yi kan rahoton kwamitinta dake kula da al'amuran INEC
- Sanata Kabiru Gaya, yace dukkan korafin da aka gabatar game da shi ba zai hana shi riƙe muƙamin ba
Majalisar dattijan ta Najeriya, ranar Alhamis, ta amince da naɗin Farfesa Sani Muhammad Adam, daga yankin arewa ta tsakiya a matsayin kwamishinan hukumar zaɓe, INEC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
The nation ta rahoto cewa, amincewa da naɗin Farfesa Adam ya biyo bayan nazari da majalisar ta yi a akan rahoton da kwamitin kula da INEC ya gabatar.
A ranar Talata da ta gabata, majalisar ta ƙi amincewa da farfesa Adam saboda wasu ƙorafe-ƙorafe da suke zagaye da shi.
Rahoton Kwamitin INEC
Shugaban kwamitin dake kula da INEC a majalisar dattijai, Sanata Kabiru Gaya, (APC, Kaduna), yayin da yake gabatar da rahoton ranar Alhamis, yace kwamitin ya gano cewa korafe-korafen dake zagaye da wanda ake son naɗawa ba gaskiya bane.
Ya ƙara da cewa duk wasu zargi da ƙorafe-ƙorafe da aka jingina masa ba zai shafi cancantarsa da muƙamin ba.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
Yace: "Kwamitin mu ya gano cewa dukkan abubuwan da ake jingina wa gare shi ba gaskiya bane, kuma ba zai hana shi yin adalci da gaskiya a muƙamin kwamishinan zaɓe ba."
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi
Shugaba Buhari zai kai ziyara jiharsa ta Katsina, inda ake tsammanin zai ƙadɗamar da wasu muhimman ayyuka.
Shugaban zai ƙaddamar da aikin ruwa na Zube Dam a Dutsinma shekara sama da 40 bayan fara shi.
Asali: Legit.ng