Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani shahararren shagon siyayya a Abuja
- Gobara ta yi kaca-kaca da wata kasuwar zamani a babban birnin tarayya Abuja a daren Asabar
- Rahoto ya bayyana cewa, har yanzu dai ba a tabbatar da mutanen da suka mutu yayin gobarar ba
- Wani shaidar ido ya bayyana cewa, tuni jami'an kashe gobara sun kawo dauki don kashe wutar
Shahararren Shagon Siyayya na Prince Ebeano da ke gundumar Lokogoma a babban birnin tarayya Abuja ya kone da yammacin ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.
Ibrahim Muhammad, jami’in hulda da jama’a na (PRO) na hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya ya tabbatar hakan a wata hira da kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi.
Wani shaidar gani da ido ya ce jami’an kashe gobara sun isa wurin kuma sun yikokarin kashe wutar, in ji SaharaReporters.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel
Muhammad ya ce, ma’aikatan kashe gobara daga ofisoshin hukumar kashe gobara da dama a Asokoro, Garki, Games Village da kuma National Judicial Institute dake Abuja sun yi kokarin kashe da wutar “mai-girma”.
A cewarsa, har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Ya ce har yanzu ba a san ko rayuka sun salwanta ba da kuma asarar dukiya da ta salwanta ba.
A cewarsa:
"Har sai bayan an kashe wutar ba za mu iya cewa ko an rasa rai ba yayin gobarar."
Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi
Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin doka da aka don bai wa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya makamai, Channels Tv ta ruwaito.
Kudirin an mika shi ne don bai wa 'yan kwana-kwana ikon daukar makamai don kare su daga hare-haren jama'a yayin da suke kan ayyukansu.
'Yan majalisar sun cire kudirin ne ta hanyar kin amincewa da kudirin da Wakili Thomas Ereyitomi ya gabatar.
KARANTA WANNAN: Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili
Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai
A wani labarin, Dakarun sojin saman Najeriya sun lalata manyan motocin bindiga guda uku mallakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP yayin da suke tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri domin aikata barna kan mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis kan ayyukan sojoji a cikin makonni biyu da suka gabata, Mukaddashin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Brig Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun kashe duk wadanda ke cikin motocin.
Onyeuko ya bayyana cewa, sojojin na sama, wadanda suka gudanar da ayyukan ta amfani da jirage masu saukar ungulu NAF Mi-35, sun yi aiki ne a lokacin da suka samu kiran gaggawa tare da tabbatar da cewa an kwato dukkanin makaman ‘yan ta’addan a yayin samamen.
Asali: Legit.ng