Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

  • Sauya shekar gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa All Progressive Congress ya haifar da karar shari'a a kotun Abuja
  • Tsohuwar jam’iyyar gwamnan ba ta ji dadin yadda ya fice daga inuwarta ba bayan da ya samu nasarar zabe
  • PDP ta zargi APC da yin amfani da halaye marasa kyau wajen samun mambobi, amma jam’iyya mai mulki ta musanta zargin

Ana iya korar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle daga mukaminsa idan har babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukunci a kan karar da ke kalubalantar sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kotun a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, ta yanke hukuncin dage karar har zuwa ranar 29 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Neja ta gyara dokar kisa, an sa hannu a fara rataye masu garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ya magantu kan tsame sunansa daga na 'yan takara a Anambra

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC
Kotun Abuja ta dage sauraro shari'ar Matawalle zuwa wata Satumba Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya yanke hukuncin ne bayan da masu shigar da kara, Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed, suka janye bukatu biyu na neman hana gwamnan da mataimakinsa ficewa daga jam’iyyar.

Kotun bata saurari karar ba kafin Matawalle ya sauya sheka.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin a sanya PDP a matsayin mai gabatar da kara sannan ya umarci jam’iyyar da ta gyara tare da gabatar da dukkan matakanta a cikin bakwai, jaridar Tribune ta ruwaito.

'Yan jam'iyyar PDP daga jihar Zamfara ne suka shigar da karar wadanda ke jin haushin cewa gwamnan ya dauki nasarar zaben da ya samu a karkashin jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Masu shigar da kara sun yi jayayya a karar su cewa gwamnan bai cancanci ci gaba da rike mukamin ba saboda sauya sheka.

Sauya sheka: Ba a tilastawa Matawalle, Ayade, da sauransu barin PDP ba, APC ta mayar da martani ga gwamnoni

Kara karanta wannan

Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna

A gefe guda, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta musanta batun tsoratar da gwamnoni daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don su fice daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyya mai mulki.

APC a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, ta hannun sakatarenta na rikon kwarya, John Akpanudoedehe, ta bayyana zargin a matsayin abin dariya da rashin gaskiya.

Gwamnonin Arewa da aka zaba a karkashin jam’iyyar adawa sun yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta tsoratar da takwarorinsu na Kuros Ribas da jihar Zamfara har sai da suka sauya sheka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng