EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta damke wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina
- Reshen rundunar ta jihar Kano ce ta yi kamun a wani samame da jami'anta suka kai karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina
- Sun kai samamen ne ne biyo bayan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu masu damfarar yanar gizo suna aikata ayyukan zamba a yankin
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Kano ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta hanyar intanet a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.
Hukumar, a cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook, ta ce wadanda ake zargin galibinsu matasa ne da shekarunsu basu wuce 20 ba.
KU KARANTA KUMA: 2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta
Ta ce:
“Wadanda ake zargin sun shiga hannun wasu jami’an hukumar ne biyo bayan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu masu damfarar yanar gizo suna aikata ayyukan zamba a kusa da karamar hukumar Dutsinma da ke jihar ta Katsina.
“A bisa karfin bayanan sirri, an tura wata tawaga ta jami’an tsaro kuma suka kai wani samame maboyarsu tare da cafke wadanda ake zargin.
“Ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.”
Sakamakon binciken da jaridar The Nation ta gudanar ya nuna cewa galibin daliban jami’a ne da matasa marasa aikin yi.
KU KARANTA KUMA: Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum
Shugaban EFCC ya yi kakkausar gargadi ga jami’an hukumar
A wani labarin, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya nemi jami’ai “masu cin hanci” da ke cikin hukumar da su yi murabus.
Yayinda yake jawabi ga ma’aikatan EFCC reshen Markurdi, babban birnin jihar Benuwe, a ranar Alhamis, shugaban ya ce dole ne a kula da kimar aiki da mutunci yayin gudanar da aiki.
Ya ce ba zai yiwu jami'in da ke aikata cin hanci da rashawa ya yaki cin hanci da rashawa ba, jaridar The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng