Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC

Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC

  • Jam’iyyar All Progressives Congress bata ji dadin yadda jam’iyyar Peoples Democratic Party ke neman gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sauka ba
  • Wani jigon jam'iyyar, Sani Shinkafi, ya zargi 'yan adawa da munafunci kan sauya shekar Bello Matawalle
  • Dan jam'iyyar APC din ya yi ikirarin cewa babu bukatar a tayar da jijiyar wuya game da ficewar gwamnan na Zamfara saboda PDP ma ta karbi masu sauya shekar a baya

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sani Shinkafi, ya yi watsi da kiraye-kirayen da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke yi na neman gwamna Bello Matawalle ya sauka.

PDP ta yi kira ga Matawalle da ya sauka daga mukaminsa na gwamna saboda sauya sheka zuwa APC, jaridar The Sun ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Cikakken jerin sunayen 'yan takarar da INEC ta tantance domin zaben gwamna

Sauya sheka: Dalilin da yasa Gwamnan Zamfara ba zai sauka daga kujerarsa ba, Jigon APC
Ana ci gaba da kai ruwa rana kan sauya shekar Matawalle Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Sai dai kuma, Shinkafi a wani taron manema labarai a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, a Abuja ya bayyana kira ga murabus din Matawalle a matsayin abin dariya.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

Jigon na APC ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyun kuma sun koma PDP.

A cewarsa, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo sun sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Ya ce:

"Muna kuma mamakin dalilin da yasa PDP wacce ta ci gajiyar sauya shekar Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da Godwin Obaseki na jihar Edo daga APC zuwa PDP, ba ta ga wani abin aibi ba game da irin wannan sauya shekar."

Babu doka a kan sauya sheka

A cewar jaridar Tribune, dan siyasan ya bayar da hujjar cewa babu wata doka da ta tilasta wani gwamna ya ci gaba da kasancewa kan mukaminsa a karkashin jam’iyyar da ya tsaya takara kuma ya ci zabe.

Shinkafi ya shawarci mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau, wanda ya ci gaba da kasancewa a PDP, da ya guji duk wani abin da zai haifar wa jihar karin matsaloli.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: Ba a tilastawa Matawalle, Ayade, da sauransu barin PDP ba, APC ta mayar da martani ga gwamnoni

Kotun Abuja ta yanke hukunci kan karar da ke neman a tsige Matawalle saboda sauya sheka zuwa APC

A gefe guda, mun ji cewa ana iya korar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle daga mukaminsa idan har babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukunci a kan karar da ke kalubalantar sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kotun a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, ta yanke hukuncin dage karar har zuwa ranar 29 ga watan Satumba.

Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya yanke hukuncin ne bayan da masu shigar da kara, Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed, suka janye bukatu biyu na neman hana gwamnan da mataimakinsa ficewa daga jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel