Gwamnatin Neja ta gyara dokar kisa, an sa hannu a fara rataye masu garkuwa da mutane
- Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello zai yaki masu garkuwa da mutane
- An sa doka domin a rataye duk wanda aka samu da laifin satar mutane a Neja
- Majalisa tayi wa doka garambawul domin a hukunta masu ba miyagu bayanai
Mai girma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sa hannu a kudirin da za ta bada dama a rika kashe masu garkuwa da mutane da barayin shanu.
A cewar jaridar The Cable, duk wanda aka samu da laifin satar mutum da nufin karbar kudin fansa a Neja, zai bakuncin barzahu ta hanyar rataye shi.
Gwamna ya sa hannu a dokar da Majalisa ta kawo masa
Abubakar Sani Bello ya ce an yi wa dokar garkuwa da mutane da satar dabbobi ta shekarar 2016 kwaskwarima domin a kashe masu ba miyagu bayanai.
KU KARANTA: EFCC ta tura ma’aikatanta, sun je wani otel sun yi ram da wasu
Duk wanda aka kama ya na taimaka wa masu garkuwa da mutane da bayanan sirri domin a saci mutum ko dabba, zai fuskanci hukuncin kisa da rataya.
Da yake bayani a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, 2021, Gwamnan ya ce za a rataye duk mai taimaka wa masu tsare mutane da dabbobin Bayin Allah.
“Dokar yanzu ta yi tanadi a kama duk wanda ya taimaka wajen satar mutum ko aka saci tumaki, ko ya taimaka da gan-gan, ko ya sa hannu wajen garkuwa da mutane ko satar dabbobi, ya aikata laifin da hukuncinsa kisa ne ta hanyar rataya.”
Kamar yadda Pulse ta rahoto, Gwamna Sani Bello ya ce wannan mataki ya zama dole ne ganin irin kalubalen da mutanen Neja su ke fuskata daga miyagu.
KU KARANTA: Irin mugun damkar da Kanu ya sha kafin a dawo da shi gida
Gwamnan na Neja ya koka game da muguwar rawar da masu taimaka wa ‘yan bindiga su ke taka wa, yace su na maida kokarin da jami’an tsaro su ke yi baya.
Sani Bello ya ce dokar da aka yi wa garambawul za ta karfafa wa ‘yan sa-kan jihar wajen yin aikin taimaka wa sauran jami’an tsaron gwamnatin tarayya.
A ranar 1 ga watan Yulin 2021, ‘yan majalisar dokokin jihar Neja su ka amince da wannan kudiri. Daga nana aka kai wa gwamna, shi kuma ya rattaba hannu.
A baya kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed ya bayyana cewa ya san wadanda ke daukan nauyin masu tada zaune tsaye a jiharsa.
Gwamnan ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa 'yan siyasa su ke kawo yan ta'adda Bauchi.
Asali: Legit.ng