Sauya sheka: Ba a tilastawa Matawalle, Ayade, da sauransu barin PDP ba, APC ta mayar da martani ga gwamnoni

Sauya sheka: Ba a tilastawa Matawalle, Ayade, da sauransu barin PDP ba, APC ta mayar da martani ga gwamnoni

  • Jam’iyya All Progressives Congress mai mulki ta yi watsi da batun cewa tana tilasta mambobin jam’iyyar PDP sauya sheka
  • John Akpanudoedehe, sakataren wucin gadi na jam’iyyar na kasa, ya bayyana zargin a matsayin abin dariya
  • Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya zargi APC da tsoratar da gwamnoni daga jam’iyyar adawa don su sauya sheka

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta musanta batun tsoratar da gwamnoni daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don su fice daga jam’iyyar adawa zuwa jam’iyya mai mulki.

APC a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli, ta hannun sakatarenta na rikon kwarya, John Akpanudoedehe, ta bayyana zargin a matsayin abin dariya da rashin gaskiya.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

Sauya sheka: Ba a tilastawa Matawalle, Ayade, da sauransu ficewa daga PDP ba, APC ta mayar da martani ga
Jam'iyyar APC ta bayyana zargin da gwamnonin PDP na arewa suka yi mata a matsayin abun dariya Hoto: @officialapcng
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa da aka zaba a karkashin jam’iyyar adawa sun yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta tsoratar da takwarorinsu na Kuros Ribas da jihar Zamfara har sai da suka sauya sheka.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba a ranar Laraba, 14 ga watan Yuli, bayan wani taro a Abuja, ya ce gwamnonin PDP da suka koma APC kwanan nan sun yi hakan ne saboda ana ci gaba da tsoratar da su.

Ya ci gaba da rokon cewa a dakatar da tsoratarwar saboda ba su da kwanciyar hankali da ita.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Neja ta gyara dokar kisa, an sa hannu a fara rataye masu garkuwa da mutane

Akpanudoedehe ya sake nanata cewa mambobin PDP da suka sauya sheka sun yi hakan ne saboda nasarorin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu daga bangarori da dama.

Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

A gefe guda, Gwamnonin Jam’iyyar PDP a Arewa suka yi zargin cewa Gwamnatin Muhammadu tana razanar da su da sauran mambobin jam’iyyar adawa domin su shiga Jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Sun yi ikirarin cewa wadansu takwarorin nasu, ciki har da Ben Ayade Gwamnan Jihar Kuros Riba da Bello Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara, wasan a kwanan baya suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki sun yi hakan ba da son ransu ba.

Gwamnonin PDPn sun kuma zargi Gwamnatin Buhari da yi wa Arewa kwange duk kuwa da cewa ita ce iko a siyasance, TheNation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel