Fashola: Ba mu da matsalar ƙarancin gidaje a Nigeria, akwai gidaje masu yawa da babu mutane a ciki

Fashola: Ba mu da matsalar ƙarancin gidaje a Nigeria, akwai gidaje masu yawa da babu mutane a ciki

  • Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce babu matsalar karancin gidaje a Nigeria
  • Fashola ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a matsayin martani kan wani rahoto da ke cewa babu isassun gidaje a kasar
  • Ministan ya ce abin da ke faruwa shine mutane suna baro gidajensu a karkara suna zuwa birane amma hakan baya nuna babu isasun muhalli

Ministan Ayyuka da Gidaje na Nigeria, Babatunde Raji Fashola, ya yi watsi da ikirari da aka yi na cewa yan Nigeria kimamin miliyan 17 fuskantar kallubalen rashin muhallai, Daily Trust ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa Fashola ya yi magana ne a ranar Alhamis yayin jawabin mako-mako da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ke shiryawa a fadar Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.

Ba mu da matsalar ƙaranci gidaje a Nigeria, In ji Fashola
Babatunde Raji Fashola, Ministan Ayyuka da Gidaje. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Ministan ya ce ya tuntubi Hukumar Kiddiga ta Kasa, NBS, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da bankin cigaban nahiyar Afirka, AfDB, kuma sun tabbatar da cewa rahoton da aka fitar kan rashin gidaje a Nigeria ba gaskiya bane.

Don haka, ya bukaci a yi watsi da ikirarin.

Ministan ya ce babu matsalar karancin gidaje a kasa kamar Nigeria da ke da gidaje da dama da babu mutane a ciki.

Ya alakanta matsin da ake samu a bangaren gidaje a kasar da tururuwar da mutane ke yi daga karkara zuwa komawa birane, hakan yasa ake samun matsalar karancin wasu abababen da ake nemansu ido rufe.

KU KARANTA: Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Fashola ya ce duba da cewa mutane sun baro gidajensu a karkara sun zo birane suna zama tare da wasu baya nufin ana fama da matsalar karancin gidaje a kasar.

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Ya ce:

"Babu hikima a ce muna da matsalar karancin gidaje idan har akwai gidaje da dama da babu mutane a cikinsu. Babu wata kasa a duniya da hakan ke faruwa."

Ya bayyana cewa ba za a san adadin karancin gidaje a kasar ba har sai an sake yin wani kidayar mutane a kasar.

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel