Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno
- Hedkwatar yaki da Boko Haram ta mika akalla mutum dubu ga gwamnatin Borno
- Hakan ya auku lokacin wani taro na sirri
- Wannan ya biyo bayan tsaresu da akayi a barikin Soji na tsawon lokaci
Hukumar Sojin Najeriya a ranar Laraba ta saki tsaffin yan Boko Haram 1,009 da suka kasance hannun Sojin a barikin Giwa dake Maiduguri, birnin jihar Borno.
An mikawa gwamnatin jihar Borno wadannan tsaffin yan ta'addan ne a wani taro na sirri da aka shirya yi a baya amma aka dage saboda mutuwar tsohon shugaban hafsin Soji, Punch ta ruwaito.
A cewar wasu majiyoyi dake cikin gidan Soja, an mika yan ta'addan ga kwamishanar harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, wacce ta wakilci gwamnatin jihar.
Hafsan yace,
"Hukumar Soji ta mika yan ta'addan Boko Haram 1,009 ga gwamnatin jihar Yau (Laraba). An yi abin a sirrance. An gargademu kada a bari yan jarida su samu shiga wajen."
Yunkurin ji ta bakin Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Col. Ado Isa, ya ci tura.
KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane
KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD
Hukumar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya
Wata sanarwa dauke da sa hannun Onyema Nwachukwu, Darakta, Jami’in Hulda da Jama’a na Soji, ta ce rahotannin karya ne kuma wani mummunan yunkuri ne na dakile tarbiyyar sojoji da kuma tozarta sojojin na Najeriya.
Yace:
“Wadannan da ake zargin an tsare su a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma karin bincike daga masana na Cibiyar Bincike ta Hadin Gwiwa (JIC).
"Kuma wadanda aka samu da laifi galibi ana mika su ga hukumomin da ke gabatar da kara a kan haka, yayin da wadanda ba su da hannu a ta’addanci da tayar da kayar baya ana wanke su kuma a sake su ga gwamnatin jihar domin gyara su kafin a maida su cikin al'umma.
Asali: Legit.ng