Jama’a sun fusata yayin da gwamnatin jihar Taraba ta fara siyar da fom din daukar aiki
- A yanzu haka akwai hargitsi a jihar ta Taraba game da sayar da fom din daukar aiki da hukuma ke yi ga masu neman aiki
- Masu ruwa da tsaki a jihar sun ce matakin ba mai karbuwa bane kuma ya kamata gwamnati ta dakatar da shi nan take
- Shugabannin Kwadago a jihar sun kuma shiga tsakani suna rokon gwamnati da ta dakatar da wannan shirin
Gwamnatin jihar Taraba ta fusata al’umman jihar kan sayar da fom ga masu neman yin aiki a ma’aikatar jihar wanda ke gudana a yanzu haka.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hukumar ma’aikatar jihar ta umarci ‘yan asalin jihar da suke da sha’awar yin aikin da su shiga tsarin neman aikin ta hanyar siyan fom a yanar gizo akan kudi N3,500.
KU KARANTA KUMA: Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna
Hukumar ta kuma umarci ma’aikatan da ke son canja ayyukansu daga karamar hukuma zuwa ma’aikatar jihar ko kuma a fadin ma’aikatu, sassa, da hukumomi da su siya fom din neman canjin wurin aiki ta hanyar biyan N3,000 a asusun gwamnatin jihar.
Gwamnatin ta gudanar da makamancin wannan shirin a shekarar 2017 amma kasa da kashi 10 cikin 100 na sama da mutane 30,000 da suka nemi aikin ne suka samu.
Wani tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) a jihar, Jonah Kataps, ya bayyana sayar da fom din neman aikin a matsayin rashin adalci.
Kataps wanda har ila yau shine shugaban kungiyar Malaman makarantu ta Najeriya kuma tsohon shugaban ma’aikatar karamar hukuma a jihar yace:
“Idan gwamnati na so ta ba marasa aiki aikin yi da gaske, me zai sa ta chaji N3,500? A yi shi a kyauta.
KU KARANTA KUMA: Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru
“Amma wannan ma ba shine babban damuwata ba. Me zai hana a fara biyan wadanda ke kasa albashi a kai a kai tare da biyansu bashin albashi sannan a fara biyan ma’aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu?"
Wani tsohon shugaban kungiyar kwadago ta ma’aikatar kananan hukumomi (NULGE) a jihar, Obidah Bitrus, yace ba daidai ba ne a chaji kudin fom din neman aiki duk da kalubalen da tattalin arzikin da kasar ke ciki a yanzu.
Kalamansa:
“Ban ga dalili da hujjar da zai sa a dauki irin wannan matakin ba. Ya kamata Gwamnati ta kula da 'yan kasarta, kar ta kara musu radadi a wannan lokaci na kalubalen tattalin arziki da tsaro inda mutane ke wahalar rayuwa."
Hakanan, shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin fararen hula na Najeriya, Gimba Joseph, ya bayyana shakkun cewa gwamnati na son yin amfani da wannan shirin don samun da kudaden shiga.
Ya ce maimakon gwamnati ta ci daga masu neman aiki, kamata ya yi ta nemi hanyoyin halal don samar da kudaden shiga.
A halin yanzu, don tabbatar da samar da aikin yi a Taraba, Hukumar Raya Kananan Masana'antu (SMEDAN), ta bude wani katafaren wurin sarrafa shayi da man zogale don karfafa tattalin arzikin mata a jihar.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Darakta-Janar na hukumar, Dr. Dikko Radda ya bayyana wannan kwanan nan a Jalingo, babban birnin jihar.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.
Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.
Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.
Asali: Legit.ng