Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi

Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi

  • Majalisar wakilai ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samar wa jami'an kwana-kwana makamai
  • Majalisar ta yi watsi da kudurin ne bayan da ta kafa hujja da cewa, jami'an kwana-kwana ba na tsaro bane
  • A baya an ruwaito cewa, an mika wa majalisa kudurin mai neman kafa wani bangare da za a kira na ''Yan Sandan Wuta'

Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin doka da aka don bai wa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya makamai, Channels Tv ta ruwaito.

Kudirin an mika shi ne don bai wa 'yan kwana-kwana ikon daukar makamai don kare su daga hare-haren jama'a yayin da suke kan ayyukansu.

'Yan majalisar sun cire kudirin ne ta hanyar kin amincewa da kudirin da Wakili Thomas Ereyitomi ya gabatar.

KARANTA WANNAN: Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi
Majalisar wakilai ta Najeriya | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, 'yan majalisar sun bayyana cewa hukumar kashe gobara ta tarayya ba ta jami'an tsaro ba ce, don haka:

Kara karanta wannan

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari

"Ba shi da ma'ana a bari ma'aikatan kungiyar su dauki bindigogi, saboda ba sa bukatar irin wadannan makamai don gudanar da aikinsu."

Mafita kan yadda jami'an kwana-kwana za su kare kansu

Maimakon ba da makamai, 'yan majalisar sun ba da shawarar a inganta aikin sosai kuma a daidaita shi don samar da aikin da ake bukata.

Kudirin an bayyana shi ne da nufin kirkirar wani bangare a ma'aikatar da zai ke daukar makamai wanda za a kira shi da "'Yan Sandan Wuta".

KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili

A baya mun ruwaito muku cewa, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kirkiro wani bangare a hukumar kashe gobara wacce za ta ba da damar daukar makami don samar da bindigogi ga ma'aikatan kashe gobara yayin gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Wannan ya biyo bayan yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na magance kalubalen da galibin ma’aikatan kashe gobara ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, ta fuskar harin tsageru da masu barnatar da kadarori a wuraren gobara a fadin kasar.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida, Misis Blessing Lere-Adams, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.