El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna za ta sake yi wa malaman frimare gwajin sanin makamashin aiki
  • Mohammed Mubarak, Jami'i daga Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar
  • Mubarak ya ce gwamnatin za ta cigaba da irin wannan gwajin domin tabbatar da samar da ilimi ingantacce a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

DUBA WANNAN: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta gwaji a Kaduna
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi biyu ne kawai ke cikin aminci a Kaduna - Sanata Sani

Ya ce dole ta sa aka dauki matakin mai wahala, yana mai cewa gwamnati ta maye gurbin malaman da ta sallama da wasu 25,000 da suka cancanta da ake yi wa tankade da reraya.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Jerin Sunayen Sakatarorin Dindindin 5 da Buhari Ya Rantsar

Ya yi bayanin cewa a yanzu hukumar na shirin yin wani gwajin sanin makamashin aiki ga malaman frimari da nufin tabbatar da samar da ilimi mai nagarta a makarantun na frimare.

Ya ce:

"Kuma a halin yanzu muna kashe Naira miliyan 341 a kan bawa malaman horaswa domin kwarewa kan aiki da tallafi daga hukumar ilimi bai daya.
"Hakan ya dace da tsarin gwamnatin jihar na tabbatar da samar da ilimi mai nagarta da koyarwa a dukkan makarantun jihar."

El-Rufai ya bada hutun kwana ɗaya a Kaduna domin zaman makokin Bantex

A wani labari daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranar Litinin 12 ga watan Yulin 2021 a matsayin ranar hutu domin karrama ayyukan tsohon mataimakin gwamna, Barnabas Yusuf Bala Bantex, wanda ya rasu a safiyar ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Sanarwar da gwamnan ya fitar da bakin mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Muyiwa Adekeye, ta ce Malam Nasir El-Rufai ya aike da sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan Bantex, Leadership ta ruwaito.

Architect Barnabas Bantex, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna a jihar Kaduna daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2019, ya rasu ne a ranar Lahadi a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel