EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

  • Hukumar EFCC ta ƙaddamar da sabuwar manhajar bankaɗo bayanan masu aikata cin hanci a Najeriya
  • Shugaban hukumar ya bayyana yadda yan Najeriya zasu tura bayanai da hotunan masu aikata laifin
  • Yace za'a iya sauke manhajar a runbun manhajoji na wayoyin Apple da kuma Android

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta ƙaddamar da wata sabuwar manhaja da zata taimakawa yan Najeriya wajen tura rahoton aikata laifin cin hanci cikin sauƙi.

KARANTA ANAN: COVID19: Wata Jami'a Ta Umarci Dalibai Su Koma Gida Har Sai Baba Ta Gani

Shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa, wanda ya ƙaddamar da 'Manhajar Eagle Eye' a Abuja ranar Laraba, yace manhajar zata ba da damar ɗaukar hotuna da wuraren da ake zargin ana aikata laifuka, kamar yadda punch ta ruwaito.

Jim kaɗan bayan kammala taron, Bawa ya shaidawa BBC hausa cewa yunƙurinsu yana cikin shirin nan na fallasa bayanai da ake kira 'Whistle Blower'

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Bawa ya ƙara da cewa duk wanda yake so ya fallasa mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki, kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai fallasa bayanai.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda ake aiki da manhajar Eagle Eye

AbdulRasheed Bawa, ya bayyana cewa masu amfani da wayoyin Apple zasu iya sauke manhajar a runbun manhajoji na App Store, yayin da masu amfani da Android zasu sauke shi daga Play Store.

Yace: "Mun sanya wa manhajar suna Eagle Eye. Za ku ga bajenmu na EFCC kamar yadda aka san shi. Idan aka duba App Store ko Google Play Store za a gan ta da suna Eagle Eye kuma za a ga EFCC a jiki."

"Idan aka sauke ta za ta yi aiki ne kamar yadda manhajar Facebook ko WhatsApp take a waya. Duk lokacin da kake son yin amfani da ita za ka buɗe ne kawai ka fara."

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

"Mutum zai iya ɗaukar hotunan gida ko wurin da ake aikata cin hanci da rashawa ya tura mana, mu kuma zamu gani mu bincike. Ba wajibi bane sai ka bayyana sunanka in kaso babu laifi."

Bawa ya kuma gargaɗi duk wanɗanda suke fallasa bayanai da su tabbatar abinda zaSu fallasa gaskiya ne.

Ya ƙara da cewa hukumar zata gayyaci wanda ya tura mata bayanan ya cike wasu takardu, da zaran an gano ƙarya yake to doka zata yi aiki akanshi.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Dan Majalisa na Shida Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC

A baya FG ta yi makamancin wannan

A shekarar 2016, gwamnatin shugaba Buhari ta kaddamar da shirin fallasa bayanai da nufin baiwa yan Najeriya damar bankaɗo ayyukan cin hanci da rashawa ita kuma gwamnati ta basu ladan aiki.

Ministan kudi a wancan zangon mulkin, Kemi Adeson, ta bayyana cewa an ƙirƙiro shirin ne domin taimakawa wajen yaki da laifin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

A wani labarin kuma Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

Wasu yan bindiga da ake zargin yan ƙungiyar ESN-IPOB ne sun kaiwa sojoji hari a jihar Enugu.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi gumurzu sosai, kuma sanadiyyar haka sojoji biyu suka rasa rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262