Cikakken Bayani: Dan Majalisa na Shida Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC
- Ɗan majalisar wakilan tarayya, Kabiru Amadu, daga jihar Zamfara ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC
- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasiƙar Amadu a zaman majalisar na Laraba
- Hon. Amadu shine ɗan majalisar wakilai na shida da ya mara wa gwamnan Zamfara baya zuwa APC
Wani ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Zamfara, Kabiru Amdu, ya sanar da zauren majalisa ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, kamar yadda punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu
Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasiƙar Hon. Amadu a zaman majalisar na yau Laraba.
Hon. Ya bayyana a cikin wasiƙarsa cewa saboda rikicin cikin gida da jam'iyyar PDP take fama da shi ne yasa ya ɗauki wannan matakin
Amadu, shine ɗan majalisar wakilai na 6 daga jihar Zamfara, waɗanda suka bayyana sauya sheƙarsu tare da gwamnan Zamfara, Bello Matawalle,.kamar yadda the nation ta ruwaito.
Babu wani rikici a PDP
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Ndudi Elumelu, ya bayyana cewa babu wani rikici a jam'iyyar PDP.
Hon. Elumelu ya sha alwashin cewa jam'iyyarsa ta PDP zata ɗauki matakin kotu a kan sauya sheƙar ɗan majalisar.
Yace: "Mai girma kakakin majalisa, babu wani rikici a jam'iyyar PDP ta jihar Zamfara."
"Kuma sashi na 68 na kundin tsarin mulki da kuma dokokin majalisa ya tanadi cewa duk wani mamba da ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya zai rasa kujerararsa."
"Amma zamu ƙalubalance hakan a kotu, kuma inada yaƙinin idan kotu ta yi hukunci zaku amince da shi."
Zamfara ta koma jihar APC
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC a hukumance a Gusau, babban birnin jihar, tare da ɗaukacin yan majalisun tarayya da na jiha.
Dukkan mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara 24, sanatoci uku, da kuma shida daga cikin yan majalisar wakilai bakwai sun marawa gwamnan baya zuwa jam'iyya mai mulki.
KARANTA ANAN: Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya
Amma har zuwa yanzun, mataimakin gwamna, Aliyu Gusau, da kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Anka/Talata-Mafara a majalisar wakilan tarayya, sun cigaba da zama a PDP.
A wani labarin kuma COVID19: Wata Jami'a Ta Umarci Dalibai Su Koma Gida Har Sai Baba Ta Gani
Jami'ar gwamnatin tarayya dake Lagos (UNILAG) ta umarci ɗalibanta su fice daga ɗakin kwanansu cikin gaggawa.
Hukumar jami'ar ta ɗauki wannan matakin ne a wani taron gaggawa da ta gudanar ranar Laraba saboda ɓarkewar COVID19.
Asali: Legit.ng