COVID19: Wata Jami'a Ta Umarci Dalibai Su Koma Gida Har Sai Baba Ta Gani
- Jami'ar gwamnatin tarayya dake Lagos (UNILAG) ta umarci ɗalibanta su fice daga ɗakin kwanansu cikin gaggawa
- Hukumar jami'ar ta ɗauki wannan matakin ne a wani taron gaggawa da ta gudanar ranar Laraba saboda ɓarkewar COVID19
- Jami'ar ta bayyana cewa duk da matakan da take ɗauka na kare yaɗuwar cutar, amma ana cigaba da samun ɗalibai na kamuwa
Hukumar jami'ar Lagos (UNILAG) ta umarci ɗalibai su fice daga ɗakin kwanan su saboda ɓarkewar cutar COVID19, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Vanguard ta rahoto cewa jami'ar ta ɗauki wannan matakin ne a taron yan majalisar makarantar wanda ya gudana ranar Laraba.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Dan Majalisa na Shida Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC
Mataimakin shugaban makarantar (VC), Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, shine ya kira taron gaggawa saboda yiwuwar ɓarkewar cutar karo na uku.
A taron, hukumar jami'ar ta amince a dakatad da lakca har zuwa 26 ga watan Yuli, inda za'a cigaba da karatu ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually).
Kulle ɗakunan kwanan ɗalibai cikin gaggawa
A wani jawabi da mai kula da al'amuran ɗalibai na jami'ar, Mr Ademola Adeleke, ya fitar, wanda akai wa take da "Garƙame wurin kwanan ɗalibai cikin gaggawa domin daƙile yaɗuwar COVID19."
Wani sashin jawabin yace:
"Domin daƙile yaɗuwar cutar COVID19 hukumar makaranta ta umarci dukkan ɗalibai su bar ɗakunan kwanan su daga 12:000 na daren ranar Alhamis 15 ga watan Yuli. Ba za'a sake barin wani ɗalibi ba bayan wannan lokacin."
"Zamu kulle ɗakunan kwanan ɗalibai har sai baba ta gani, sabida haka kowane ɗalibi ya ɗauke kayayyakinsa ya koma gida."
"Za'a cigaba da karatu ta hanyar amfani da fasahar zamani ta yanar gizo-gizo wato (Virtually) daga ranar 26 ga watan Yuli."
Ko za'a dawo karatu nan kusa a UNILAG?
A wani jawabi na daban da shugaban sashin yaɗa labarai na jami'ar, Mrs Nonye Ogwuma, ta fitar, ta bayyana cewa mai yuwu wa a dawo da karatu yadda aka saba a ƙarshen watan Mayu idan aka samu nasarar rage yaɗuwar cutar da kashi ɗaya.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu
Tace duk da bin matakan kare yaɗuwar cutar da hukumar UNILAG ta yi, da kuma samar da allurar rigakafinta, amma an cigaba da samun ɗaliban da suka kamu da ita.
"Yana yin ya zama a bun damuwa matuƙa, shiyasa aka kira taron gaggawa. Inda aka amince kowane ɗalibi ya fice daga ɗakin kwanan ɗalibai daga 12:00 na daren Alhamis." a cewarta.
A wani labarin kuma Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya
Wata santaleliyar yar ƙasar Amurka ta bayyana sabon sunan da ta canza bayan ta yi wuf da ɗan Najeriya.
Matar mai suna, Janna Mofeyisola, ta canza sunan zuwa irin na yaren mijinta, Janna Ikuejamoye.
Asali: Legit.ng