Bikin Babbar Sallah: Mutane sun Koka Kan Yadda Farashin Dabbobin Layya Ya Yi Tashin Gwauron Zabi
- Yayin da bikin babbar sallah yake ƙara matsowa, mazauna garin Kano sun fara kokawa kan tashin farashin dabbobi
- Rahoto ya nuna cewa farashin rago, tumaki, shanu ya ƙaru sosai idan aka haɗa da farashin su na bara
- Yan kasuwa sun bayyana cewa ba laifinsu bane, domin suna wa dabba farashi ne dai-dai da yadda ya iso gare su
Mazauna garin Kano sun koka da tashin farat ɗaya da farashin rago, shanu da akuya kwanaki kaɗan kafin bikin sallah babba (Eid-el-kabir), kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Halin Ƙuncin da Aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa farashin dabbobin ya tashi sosai idan aka haɗa da farashin su a shekarar da ta gabata.
Alhaji Muslimu Abdulhamid, wani mai sana'ar siyar da rago, yace:
"Ragon da aka siyar N30,000 a shekarar da ta wuce, bana ana siyar da shi tsakanin N55,000-N65,000, na N50,000 ya koma N100,000-N120,000."
"Hakanan kuma ragon da aka siyar bara a farashin N80,000-N90,000, a bana ana siyar da shi a tsakanin N170,000-N200,000."
Masu buƙatar dabbobin, sun bayyana cewa wannan tashin farashin cikin ƙanƙanin lokaci zai iya shafar ƙoƙarin su na yin layya da babbar sallah.
Mutane sun yi ƙorafin tashin farashin dabbobin layya
Da yake magana game da lamarin farashin, Malam Ali Muhammad, ya yi ƙorafin cewa ya ƙaraɗe kasuwa na tsawon awanni domin ya samu rago ɗan dai-dai amma abun ya gagara, babu wani zaɓi da ya wuce a siya a yadda farashin yake.
Wani dake son ya siya rago, Ibrahim Bashir, ya bayyana cewa ya zame masa dole ya jira zuwa gab da sallah kafin ya siya ragon, da fatan farashin zai sauka kafin lokacin.
Ko menene dalilin tashin farashin lokaci ɗaya?
A ɗaya ɓangaren kuma, masu kasuwancin dabbobin sun alaƙanta tashin farashin da ƙaruwar kuɗin kawo dabbobin zuwa Kano.
Wani mai saida raguna a kasuwar dabbobi ta kwanar Badawa, Alhaji Ibrahim Ahmad, yace kuɗin kawo dabbobi cike da babbar motar ɗaukar kaya daga Ganda, jihar Yobe, zuwa Kano ya tashi daga N150,000-N200,000.
Ibrahim, yace: "Ba hakanan muka ƙara farashin ba, muna siyar wa ne dai-dai da yadda suka iso gare mu."
"Muna kawo dabbobi daga ƙasashen dake maƙwaftaka da mu, saboda munsan abunda muke da shi a ƙasa ba zai isa buƙatar mu ba."
KARANTA ANAN: Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna
Tashin farashin ya shafi rashin saye dabbobin
A nashi ɓangaren, Malam Safiyanu Musa, wani mai kasuwancin rago a kasuwar Yan Awaki, Tashamu, yace tashin farashin rago ya shafi kasuwancin sa.
Ya kara da cewa yanzun rago biyu kacal yake siyarwa a rana amma a bara kuwa yakan saida 10-15 a rana ɗaya.
A wani labarin kuma An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu
Yan bindiga sun kaiwa ɗaliban jami'ar jihar Delta hari yayin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.
Maharan sun kashe ɗalibi ɗaya, Odje Stephen, sannan suka yi awon gaba da wasu guda biyu, Jennifer da Divine.
Asali: Legit.ng