Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya lallashi wasu mutanen jiharsa kan yadda hanyoyi suka lalace
  • Gwamnan ya yi wannan magana ne yayin da yake kaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya biyo wasu hanyoyi kuma yaji irin zafin da mutane suke ji idan suka bi hanyoyin

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya lallashi mazauna jiharsa bisa yanayin baƙin ciki da rashin kyau na hanyoyi a jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bikin Babbar Sallah: Mutane sun Koka Kan Yadda Farashin Dabbobin Layya Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Gwamnan yayi magana ne yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen ƙananan hukumomin dake tafe a ƙaramar hukumar Imeko Afon, jihar Ogun.

Gwamnan ya yi alƙawarin sake gina hanyar Abeokuta-Olorunda-Imeko, wacce ta zama wurin aikin masu garkuwa da mutane a jihar.

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun
Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Naji raɗaɗin da kuke ji

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Da yake jawabi ga mutanen ƙaramar hukumar Imeko Afon, gwamnan yace gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan cigaba kala daban-daban guda 52 a yankin su cikin shekaru biyu.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i

Gwamnan yace: "Gwamnatin ku ce, ku cigaba da taimaka mana da addu'a. A kan hanyata ta zuwa nan daga Abekuta, na biyo ta Lafenwa zuwa Rounda da Olorunda, har na iso nan, naga yadda hanyoyin suka lalace kuma naji irin zafin da kuke ji."

"Na muku alƙawari yau cewa kafin in sake zuwa nan gaba, wannan hanyar an kammala ta ko ana gab da haka."

A wani labarin kuma Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta fitar da rahoton adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin yan bindiga cikin watanni uku.

Kara karanta wannan

Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Ma'aikatar tsaro da al'amuran cikin gida ta bayyana cewa an kashe mutum 222 da yan bindiga 87.

Asali: Legit.ng

Online view pixel