Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i

Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i

  • Gwamna El-Rufa'i na Jihar Kaduna ya bayyana cewa ya damu matuƙar damuwa da halin ƙuncin da jama'a suke ciki
  • Gwamnan yace rahoton tsaro da aka gabatar ya nuna ainihin baƙin ciki da takaicin da rashin tsaro ya jawo
  • Ya tabbatar wa al'ummar Kaduna cewa gwamnati na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya a jihar

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya bayyana cewa yana cikin matuƙar damuwa saboda halin ƙunci da al'umar Kaduna suke ciki wanda matsalar tsaro ta haifar a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna

A jawabin da gwamnan yayi lokacin gabatar da rahoton tsaro kashi na 2 a cikin 2021, El-Rufa'i yace wannan rahoton ya bayyana komai game da halin da mutane suke ciki.

"Wannan adadin da rahoton tsaro kashi na 2 a cikin 2021 ya gano, ya nuna ƙarara irin halin ƙuncin da al'umma suke ciki, baƙin ciki, rashin yan uwansu da tsoron da aka jefa su a ciki," inji gwamnan.

Kara karanta wannan

Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Watanni 3 a Kaduna

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i
Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Gwamanan ya kuma bayyana cewa rahoton ya bayyana abinda gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro suke yi domin daƙile lamarin.

Zamu cigaba da taimakawa jami'an tsaro

El-Rufa'i ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na cigaba da taimakawa hukumomin tsaro da iyakar abinda zata iya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Hakanan, ya bayyana cewa ya kai kokensa ga gwamnatin tarayya domin a haɗa karfi da ƙarfe wajen kawar da duk wani ƙalubalen tsaro a jihar.

Ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu

Gwamnan ya roƙi sarakunan gargajiya da mutanen da suke mulka musamman na ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Jema'a, da cewa kada su dogara da jami'an tsaro kaɗai don zaman lafiyarsu.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Dumi: An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu

Ya kuma yi jimami da ta'aziyya ga mutane da jami'an tsaro bisa halin ƙunci da baƙin cikin wanda yanayin ya jefa su a ciki.

Kara karanta wannan

COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola

"Ina mai tabbatar muku muna aiki ba dare ba rana domin warware wannan matsalolin, kuma aikin mu ne mu yi hakan." inji gwamnan.

A wani labarin kuma Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Sanatoci zasu gyara wasu dokokin hukumar JAMB domin inganta ɓangaren ilimi a Najeriya.

Kwamitin ilimi na majalisar dattijai ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai hukumar JAMB.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262