Da dumi-dumi: Jerin sunayen kwamishinonin INEC 5 da majalisar dattijai ta tabbatar da su
- Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wasu mutane biyar a matsayin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
- Wadanda aka tabbatar sune Farfesa Muhammad Sani Kallah; Farfesa Kunle Ajayi, Saidu Ahmad, Baba Bila da Abdullahi Zuru
- Har ila yau majalisar ta ki tabbatar da Farfesa Sani Adam daga Arewa ta Tsakiya saboda koke-koken da ake yi a kansa
Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Kwamishinoni biyar a hukumar zaben kasar, jaridar Punch ta ruwaito.
An tattaro cewa majalisar tarayyar ta tabbatar da zabin na Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, a ranar Talata, 13 ga watan Yuli.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro
Jerin sunayen kwamishinonin kasar da aka tabbatar
1. Farfesa Muhammad Sani Kallah (Katsina)
2. Farfesa Kunle Ajayi (Ekiti)
3. Saidu Ahmad (Jigawa)
4. Baba Bila (Arewa Maso Gabas)
5. Abdullahi Zuru (Arewa maso Yamma).
A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa, bayan shawarar da kwamitinta ya bayar, ta ki tabbatar da Farfesa Sani Adam daga Arewa ta Tsakiya saboda koke-koken da ake yi a kansa.
Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC
A baya mun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.
An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.
Asali: Legit.ng