N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran

N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran

  • EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero tare da wasu a gaban wata babban kotun tarayya
  • Kamar yadda lauyan masu kara ya sanar, ana zargin Ramalan tare da wasu da karbar N7m daga Diezani domin juya zaben shugaban kasa
  • Sai dai kotun ta ce za ta dasa daga inda aka tsaya a wancan gurfanarwan kuma za ta cigaba da shari'ar a watan Oktoba mai zuwa

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a ranar Talata ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero a gaban Mai shari'a M.G Umar na babban kotun tarayya a Kaduna kan zargin laifuka takwas.

EFCC tana bincikar Yero tare da Nuhu Somo Wya, tsohon minista, Ishaq Hamsa, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna da Abubakar Gaiya Haruna tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar kan zarginsu da raba kudi har naira miliyan bakwai wanda tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison-Madueke ta bada domin juya sakamakon zaben shugaban kasa na 2015.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

KU KARANTA: Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama

N700m na rashawar Diezani: EFCC za ta sake gurfanar da Yero tare da sauran
N700m na rashawar Diezani: EFCC za ta sake gurfanar da Yero tare da sauran. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

Sake gurfanar da su a ranar Talata ya biyo bayan mayar da alkali mai shari'a, Jastis Zainab B. Abubakar zuwa wata babbar kotun tarayya, Punch ta ruwaito.

A lokacin da aka kira shari'ar, lauyan masu kara, Nasiru Salele ya sanar da kotun cewa an sake gurfanar da wadanda ake zargi ne kuma yayi kira ga kotun da ta cigaba da shari'ar.

Amma kuma lauyan wadanda ake kara ya janyo hankalin kotun kan cewa a baya an bada belin wadanda ke kare kansu don haka ta dasa daga inda aka tsaya, lamarin da lauyan masu kara bai soka ba.

Daga bisani kotun ta amince da belin wadanda ake zargin kuma ta dage shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Oktoba mai zuwa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

A wani labari na daban, bayan sa'o'i ashirin da hudu da sace Sarki Alhaji Alhassan Adamu na Kajuru, 'yan bindiga sun sako shi tare da mika shi ga iyalinsa.

A ranar Lahadi, wasu miyagun 'yan bindiga sun shiga har cikin gidan sarautar Kajuru inda suka sace sarki tare da wasu mutum 13.

Sai dai 'yan biindigan sun sako sarkin tare da rike gimbiya daya da sauran wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: