Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari

Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari

  • Shugaba Buhari ya karbi bakuncin yan majalisar wakilan tarayya
  • Mambobin majalisar sun gudanar da taron tattauna matsalar tsaro a Najeriya
  • Sun gabatarwa Buhari rahoton abubuwan da suka tattauna

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana mamakin yadda yan Najeriya suka amince suka zabeshi duk da cewa bai da kudi.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da ya karbi rahoton tsaro na taron matsalar tsaron da majalisar wakilai ta gudanar ranar 26 ga Mayu.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya jagoranci tawagar yan majalisar wajen mikawa Buhari rahoton.

Buhari ya ce dubi ga irin goyon bayan da yan Najeriya suka yi masa, ya zama wajibi yayi musu aiki.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari
Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

Yace:

Kara karanta wannan

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

"Adadin mutanen da suka fita gani na. sukayi tsayuwan awanni 10 a rana, ya fi karfin abinda wani zai saya da kudi, ko karfi."
"Kawai don suna son ganin waye Buhari. Mutane na mamakin yadda yan Najeriya suka karbeni, duk da cewa bani da kudi. Nima ina mamaki."
"Hakan ya sa na ga wajibi ne in yi iyakan kokarina ga Najeriya

Shugaban kasan ya kara da cewa yan Najeriya su godewa Allah kasar bata rabe ba duk da kalubalen da ake fama.

Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah

Bishop na Katolika na yankin Sakkwato, Matthew Kukah, ya shaida wa Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka cewa Gwamnatin Tarayya ba ta iya yin komi game da matsalolin tsaro, wanda ta yi alkawarin magancewa kafin ta karbi mulki a 2015.

Ya fadi hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi game da yadda kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Arewa ke muzgunawa Kiristoci a Najeriya, ga Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Tom Lantos da ke Washington, DC, a Amurka.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng