Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

  • Gwamna Bala Mohammed yace yan siyasan Abuja na kokarin ganin bayansa
  • Bala yace yan siyasa ke shigo da masu tada zaune tsaye cikin jiharsa
  • Ya lashi takobin tona asirinsu idan lokaci yayi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed AbdulKadir ya bayyana cewa ya san wadanda ke daukan nauyin masu tada zaune tsaye a jiharsa.

Gwamnan wanda yayi wannan furuci yayin rabawa mutane kudin jari a karamar hukumar Darazo na jihar ranar Talata ya lashi takobin tona asirin masu daukar nauyin hare-hare a lokacin da ya dace, rahoton DailyTrust.

Ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa yan siyasa ke kawo yan ta'adda jihar.

Yace:

"Ina son mutanemu su kasance tare, muyi watsi da jita-jita, kiyayya da zamba. Kada ku saurari yan siyasan Abuja da basu da wani abun yi illa kokarin ganin bayan Bala Mohammed."
"Da ikon Allah, na zama gwamna da su ko ba su, zan rayu zuwa lokacin da Allah ya yanke min. Zan iya neman tazarce, da yiwuwa ma ba zan rayu zuwa lokacin ba; zan iya neman shugaban kasa, babu abinda zasu iya yi. Na san abin da suke yi."

"Na san abinda wasu yan siyasa suke yi na shigo da yan ta'adda jihar. Zan yi magana idan lokaci yayi. Ba tsoronsu muke ba."
"Kun ga abinda ke faruwa a Bauchi kwanakin nan, ta'addanci, sace-sace da garkuwa da mutane. Mun san masu daukar nauyinsu."

KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Gwamnan jihar Bauchi
Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane Hoto:PR
Asali: UGC

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa

A bangare guda, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin gwamnatinsa na KEEP.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Legit ta samu daga Lawal Muazu Bauchi mai tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani.

Ya ce yayin bikin mika kayayyakin da suka hada da jari, motoci da babura, injin markade da sauransu wa al'umar kananan hukumomin Gamawa da Zaki, gwamnan yace gwamnatinsa ta ware kimanin naira biliyan daya da miliyan dari biyar don bada jari da horaswa kan sana'oin hannu a fadin jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel