Wata sabuwa: Ana kyautata zaton dage sauraran shariar Nnamdi Kanu saboda wasu dalilai

Wata sabuwa: Ana kyautata zaton dage sauraran shariar Nnamdi Kanu saboda wasu dalilai

  • Rahoto ya bayyana cewa, babbar kotun tarayya za ta shiga hutun shekara-shekara gabanin saurarar shari'ar Kanu
  • Wata sanarwar da aka fitar, ta bayyana ranar da za a shiga hutun, tare da bayyana ranar dawowa
  • Wannan yasa ake kyautata zaton shugaban kungiyar IPOB zai iya ci gaba da kasancewa a garkame

Shugaban kungiyar IPOB na iya ci gaba da kasancewa a tsare a hannun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya har zuwa watan Satumba yayin da alkalan babbar kotun tarayya za su fara hutun su na shekara-shekara a ranar 26 ga watan Yuli, ranar da aka sanya don sauraren kararsa.

Hutun alkalan zai ci gaba har zuwa 17 Satumba, 2021, Punch ta ruwaito.

Babban jami’ar yada labarai na Babbar Kotun Tarayya, Catherine Christopher, ce ta bayar da sanarwar hutu a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Jami'ar ABU Zaria Ta Sanar da Ranar Koma Wa Karatu Gada-Gadan Bayan Janye Yajin ASUU

KARANTA WANNAN: Gwamnan Gombe ya bayyana matakan da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Ana kyautata zaton dage sauraran karar Nnamdi Kanu saboda wasu dalilai
Nnamdi Kanu shugaban IPOB | Hoto: gettyimages
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin sanarwar ya ce:

"Dangane da tanadin Doka ta 46, Doka ta 4 (d) na Dokokin Babban Kotun Tarayya (Dokar Farar Hula) na 2019, Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayyar Najeriya, Mai Shari'a John Terhemba Tsoho, yana sanar da Alkalai, masu ruwa da tsaki da sauran jama'a, cewa Babbar Kotun Tarayya za ta shiga hutun ta na shekara-shekara na shekarar 2021 daga Litinin 26 ga Yuli, 2021 zuwa Juma'a 17 ga Satumba, 2021.
"Kotun za ta ci gaba da zama a ranar Litinin 20 ga Satumba, 2021."

A cewar sanarwar, hutun shekara ta 2021 ya zama dole ga alkalai su huta kuma su shirya sabuwar shekarar doka.

Sanarwar ta kuma ce, manyan sassan Abuja, Lagos da Fatakwal ne kawai za su ci gaba da aiki a tsawon lokacin hutun.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Alkalan da za zasu zauna a tsawon lokacin hutun sune Justice A. R. Mohammed da Justice O.E. Egwuatu na sashen Abuja; Justice I. N. Oweibo da Justice Tijjani Ringim na reshen Legas; da Justice S. D. Pam da Justice A. T. Mohammed na sashen Port Harcourt.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa a lokacin hutun ba kowace irin kara za a saurara ba.

A baya mun ruwaito muku cewa, an dage saurarar shari'ar Nnamdi Kanu din daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Yulin bana.

Rahotanni Sun Bayyana Yadda Aka Kamo Nnamdi Kanu a Wata Kasar Turai

Wani rahoto na jaridar Daily Sun ya nuna cewa an kama Mazi Nnamdi Kanu a Jamhuriyar Czech.

A cewar rahoton, shugaban IPOB ya yi tafiya daga kasar Ingila zuwa Singapore saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba kafin ya tafi Jamhuriyar Czech a ranar Juma’ar da ta gabata, 25 ga Yuni.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Rahoton ya ambato wata majiya, inda ya ce akwai wani bayani da jami'an Jamhuriyar Czech suka ba gwamnatin Najeriya, wanda ya kai ga kame Kanu a birnin Prague.

KARANTA WANNAN: Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

A wani labarin, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli ya mayar da martani ga matsayar kungiyar koli ta zamantakewar al'adun Ibo, Ohanaeze Ndigbo, na sanya ido kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Malami, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Umar Gwandu kuma Legit.ng ta gani, ya yi maraba da kafa kungiyar lauyoyin da kungiyar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel