Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili

Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta ce za ta samar da bindigogi ga ma'aikatan kashe gobara a Najeriya
  • Gwamnati ta bayyana dalilin haka da cewa, zai taimaka su ci gaba da aiki yadda ya kamata
  • Ta kuma bayyana cewa, ma'aikatan na fuskantar kalubale wajen gudanar da ayyukansu a fadin kasar

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kirkiro wani bangare a hukumar kashe gobara wacce za ta ba da damar daukar makami don samar da bindigogi ga ma'aikatan kashe gobara yayin gudanar da ayyukansu.

Wannan ya biyo bayan yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na magance kalubalen da galibin ma’aikatan kashe gobara ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, ta fuskar harin tsageru da masu barnatar da kadarori a wuraren gobara a fadin kasar.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida, Misis Blessing Lere-Adams, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Abuja.

KARANTA WANNAN: Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara

Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindigogi
Rauf Aregbesola, Ministan cikin gida | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar ta, Ministan cikin gida, Cif Rauf Aregbesola da Shugaban Hukumar, sun bayyana hakan a lokacin bikin bude Majalisar Kashe Gobara ta Kasa a birnin Jos, Punch ta ruwaito.

Ministan ya samu wakilcin Babban Sakatare a ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore.

Aregbesola ya ce ma'aikatar za ta fara aiwatar da tsarin soke dokar hukumar kashe gobara ta 1963 da ba za ta yi aiki ba tare da samar da sabuwar doka ta zamani, mai karfi da kuma tilasta aiki, ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa.

In ji shi, za a tura batun ga Majalisar Dokoki ta Kasa don tattaunawa a karshe kuma ta zama doka.

Ya lura cewa kula da gobara, muhimmin abu ne ga tsaron kasa, wanda ya kamata ya zama kayan aiki ba wai kawai tsaron kasa kadai ba, har ma da ci gaban kasa.

“Lokacin da aka kare mahimman kadarorin kasa yadda ya kamata daga babbar asara sakamakon tashin gobara, an kare wadannan kadarori.

Ministan ya tabbatar cewa, Ma’aikatar za ta ci gaba da nemo sabbin hanyoyi da dabaru da za a karfafa aikin don samar da ingantaccen aiki a kan kari ga 'yan kasa baki daya.

Hukumar kashe gobara ta tarayya, ya lura, ta samu goyon baya, kuma za ta ci gaba da samun gagarumar goyon bayan Shugaba Muhamadu Buhari, in ji rahoton The Nation.

KARANTA WANNAN: Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

Yadda Tankar Gas Ta Fadi a Kasuwa, Ta Yi Kaca-Kaca da Mutane 10

A wani labarin daban, Wata tankar dakon gas ta murkushe mutane 10 tare da jikkata wasu a wata kasuwa a garin Ibadan.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa motar ta kwace wa direban ne a kusa da yankin Idi Arere kuma ya yi ta kokarin sarrafata har sai da ta isa Kasuwar Bode.

An ce jami'an kashe gobara sun isa wurin don hana tankar da ta kife daga fashewar da kamawa da wuta.

Amma mazauna garin sun ce har yanzu suna cikin yanayin tsoro saboda yiwuwar fashewar wani abu daga tankar.

Wani shaidaN gani da ido ya fadawa SaharaReporters cewa hukumomin tsaro sun mamaye kasuwar domin kwashe gawarwakin wadanda hadarin ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel