Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahra Buhari

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahra Buhari

  • Daya daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra Indimi, ta yi karin haske game da zamantakewar aure
  • A cewar 'yar shugaban kasar, matar mutum ita ce mutum mafi kusanci gare shi wacce za ta iya tabbatar da ko shi mutumin kirki ne
  • Zahra ta bayyana hakan ne a dandalin sada zumunta ta shafinta na Instagram sannan daga bisani masu amfani da intanet suka mayar da martani game da sakon bayan abun ya yadu a yanar gizo

Daya daga cikin ‘ya‘ yan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Indimi, ta haddasa cece-kuce a yanar gizo bayan ta bayyana ra’ayinta kan yadda ake tantance abokin zama nagari.

A wani wallafa da matashiyar tayi a shafinta na Instagram, ta wallafa wani bidiyo na wani malami da ke magana kan koyarwar Annabi Muhammad.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

A cewar malamin, mafi alkhairi a cikin mutane sune wadanda suke kyautata wa abokan zamansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Daga nan Zahra ta bayan sakon da tsokaci inda ta bayyana cewa abu ne da ta dade da yarda da shi.

Da take ci gaba da bayani, matashiyar ta ce matar mutum ce mafi kusanci da su kuma idan har za su iya ba da shaidar nagartarsu, to gaskiya ne.

Kalli hotunan wallafarta a kasa:

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari
Zahra Buhari ta ce matar mutum ce za ta iya fadin halayyarsa ta gaskiya Hoto: @mrs_zmbi
Asali: Instagram

Kalli wallafar a kasa:

'Yan Najeriyar sun maida martani

Ba da jimawa ba jawabin ya yadu a shafukan sada zumunta kuma yan Najeriya masu amfani da intanet sun bayyana ra’ayinsu kan lamarin. Wasu daga cikinsu sun tambaya ko mahaifiyarta ta yarda da mahaifinta, Shugaba Buhari shima mutumin kirki ne. Karanta abin da wasun su suka ce a kasa:

KU KARANTA KUMA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Vintagewearl:

"Mahaifiyarki ta sha faɗin cewa mahaifinku ba mutumin kirki bane."

Kara karanta wannan

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Seundreams:

"Shin Aisha mahaifiyarki zata iya faɗin haka ga mahaifinki? Mtchew."

Pretty_rose935:

"Haka ne, budurwarka, matarka ita ce kadai za ta iya fadin ko kai mutumin kirki ne ko na banza. Wasu mutane suna da kirki a waje yayin da suke zama azzalumai a cikin gida.
Kada wanda ya yanke hukunci kan wannan kyakkyawar matashiyar, ba ita ce Buhari ba."

Legendary_e.e:

"Wannan yana nufin Mahaifiyarki tayi gaskiya game da Mahaifinki."

An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

A wani labari makamancin haka, Zahra ta sanya mutane a shafukan sada zumunta tattaunawa bayan ta yi wani wallafa inda ta bayyana abin da aure yake nufi a gare ta.

Zahra ta wallafa wani bidiyo inda ta tara mutane da dama don bayyana ra'ayinsu game da aure. Yayin da wasu daga cikinsu suka bayyana shi a matsayin mai ban sha’awa, wasu kuma sun ce aure na nufin yarda da sauransu.

Kara karanta wannan

ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

A rubutun da ke kasan wallafar, matashiyar ta bayyana nata ra'ayin kan lamarin. A cewar Zahra, aure a gareta yana nufin soyayya mara iyaka ta kowane siga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel