Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

  • Tsohon kakakin majalisar wakilai a Najeriya ya goyi bayan kame Nnamdi Kanu da farautar Sunday Igboho
  • Rahoto ya bayyana cewa, Ghali Na'Abba ya ce babu wani dan Najeriya mai kishin kasa da zai goyi bayan ta'addanci
  • Hakazalika ta yi watsi da batun sakataren kungiyar NCFront na cewa kungiyar za ta kare hakkin Yarbawa

Ghali Na’Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da kuma Sunday Igboho, dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, The Cable ta ruwaito.

Na’abba, wanda shine shugaban kungiyar tuntuba ta Najeriya (NCFront), ya fadi hakan ne a matsayin martani ga wata sanarwa daga Olawale Okunniyi, sakataren kungiyar.

Okunniyi ya ce NCFront za ta kare Yarbawa masu zanga-zanga a kotu, biyo bayan kame wasu adadi na masu zanga-zangar a karshen mako a jihar Legas.

KARANTA WANNAN: Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina

Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho
Tsohon kakakin majalisa, Ghali Na'Abba | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

NCF Na goyon bayan gwamnatin tarayya, ba ta goyon bayan ta'addanci

Amma Na’abba a ranar Litinin, ya ce bayanin Okunniyi na kashin kansa ne domin shi da mafi yawan mambobin kungiyar suna goyon bayan matakin gwamnati.

A cewar Daily Trust, Na'Abba ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakin da ya dace na kame su kuma kungiyar ta NCFront ba za ta buya a bayan hakkin bil adama ba don kare "'Yan ta'adda".

A cewarsa:

“Batun Kanu da Igboho na da sarkakiya sosai. Sai dai, na yi imanin abinda gwamnati ta yi ta hanyar bikame su kusan kowane ɗan Najeriya na goyon bayan hakan. Babu wani a kasar nan da za a bari ya aikata wadannan abubuwa.”

“Saboda haka, gwamnati na da cikakken goyon baya daga kaina da kuma yawancin membobin kwamitin gudanarwa na NCFront. Don haka, abinda sakatare na kasa ya fada ra'ayinsa ne, babu wanda ya goyi bayansa musamman ma ni kaina.

“Ba ma goyon bayansu, muna goyon bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka. Ba za mu goyi bayan wani abu da zai cutar da kasa ba.
"Ba za mu buya ba a bayan batun kare hakkin dan adam ba don kare 'yan ta'adda, mutanen da ayyukansu suka zama barazana ga doka da oda a kasar."

An kama Kanu tare da dawo da shi Najeriya a watan Yuni don fuskantar shari'a bayan ya tsallake belinsa ya gudu daga kasar a shekarar 2017.

Hakazalika, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fara farautar Igboho bayan ya tsere daga kamun da aka yi masa lokacin da suka afka gidansa a jihar Oyo a ranar 1 ga watan Yuli.

KARANTA WANNAN: Jihar Legas za ta sanya dokar hana gabatar da wadanda aka kame da laifi a gaban 'yan jarida

A wani labarin, Jihar Osun - Sarkin gargajiya, Olowu Kuta kuma Shugaban Majalisar koli ta Owu Obas, Oba Hameed Makama, ya shawarci mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Ighoho, da ya mika kansa ga Ma’aikatar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa dake Owu Kuta a karamar hukumar Aiyedire a jihar Osun yayin hira da manema labarai.

Ya shawarci masu fafutukar ballewar da su tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.