‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

- An samu hatsaniya, a Ikotun dake jihar Legas, inda wasu masu luwadi sukayi fada da junansu bayan kmauwa da cutar kanjamau

- Ezeugo daya daga cikin masu luwadin shine ya sanyawa masoyin nasa cutar, bayan ya kawo wani zaiyi luwadin dashi sai na farkon ya tayarda da hayaniya

- Mutanen Unguwa dole tasa suka kirawo jami’an ‘Yan Sanda na Ikotun, inda suka kama wadanda ake zargin

An samu hatsaniya, a Egbe, Ikotun dake jihar Legas, inda wasu masu luwadi sukayi fada da junansu bayan kmauwa da cutar kanjamau.

Ezeugo daya daga cikin masu luwadin shine ya sanyawa masoyin nasa cutar, bayan ya kawo wani zaiyi luwadin dashi sai na farkon ya tayarda hayaniya a cikin gidan da misalin karfe 3 na dare a ranar Talata.

Mutanen Unguwa dole tasa suka kirawo jami’an ‘Yan Sanda na Ikotun, inda suka kama wadanda ake zargin. Inda Ezeugo ya masawa hukumar ‘Yan Sanda cewa ya kai shekara biyar yana luwadi.

‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas
‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a SP Chike Oti, yace wadanda ake zargin sun kaure da fadan ne bayan sun gane cewa duk sun kamu da cutar kanjamau. Ya kuma bayyana wadanda ake zargin wadanda shekarunsu basu wuce 20 zuwa 31, Ezeugo, Akachukwu, Abuchi, Dara da kuma Marvellous.

KU KARANTA KUMA: Dasuki yayi karar Malami da hukumar SSS, ya bukaci 5bn saboda sun tsareshi ba bisa ka’ida ba

Ya kara da cewa yanzu haka suna tsare a hannun hukumar ‘Yan Sandan kuma suna taimakawa da bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng