Rashin tsaro a Najeriya: Wasu 'yan bindiga sun kashe malamin addini a jihar Taraba
- Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe wani malamin addini, Timothy Damisa a jihar Taraba a cewar wani rahoton manema labarai
- A cewar matar Damisa, an harbe malamin a gabanta lokacin da ‘yan ta’addan suka mamaye gidansu da misalin karfe 2:00 na tsakar dare
- Da take ci gaba da bayani, matar ta bayyana cewa masu laifin ba su nemi komai ba yayin da suka mamaye gidansu
An kashe Timothy Damisa, wani malamin addini a Baissa, karamar hukumar Kurmi ta jihar Taraba.
An tattaro cewa maharan sun harbe Damisa wanda ya kasance limamin cocin 'Christian Reformed Church in Nation (CRCN)' sau da dama a gidansa da safiyar ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli, jaridar Premium Times ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello
A cewar matarsa, Rahab Damisa, makasan sun afka gidan ne da misalin karfe 2:30 na tsakar dare sannan kuma suka harbe mijinta har lahira a gabanta.
Ta ce:
"Lokacin da suka zo da yawansu, sai suka ci gaba da harbe-harbe don tsoratar da dukkan jama'ar yankin sannan suka kutsa kai cikin gidanmu. Maharan ba su nemi kudi ko wani abu ba kafin su harbi mijina sau da yawa."
KU KARANTA KUMA: Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba
Ta ce nan take suka tafi bayan sun tabbatar ya mutu.
Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 9
A wani labarin kuma, wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun sake kai hari ƙauyen Makarau Jankasa, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe aƙalla mutum 9, kamar yadda leadership ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa mafi yawan mazauna ƙauyen sun tsere daga gidajensu zuwa ƙauyukan dake maƙwaftaka da su.
Wannan sabon harin na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Warkan dake ƙaramar hukuma ɗaya da wannan, inda aka kashe mutum 9 tare da jikkata wasu da dama, kuma aka ƙona gidaje 12, kamar yadda punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng