Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba

Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi ikirarin ba zai taba komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC ba
  • Gwamnan yace jam'iyyar PDP kaɗai zata iya warware matsalolin da gwamnatin APC ta jefa Najeriya a ciki
  • Ya kuma yi kira ga yan Najeriya su yi rijista da jam'iyyar PDP, yayin da ta ƙaddamar da shirin rijista ta yanar gizo

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya sha alwashin ba zai taɓa komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi

Gwamnan ya fice daga jam'iyyar APC a shekarar 2020 bayan ya gaza samun tikitin sake tsayawa takara a karo na biyu.

Gwamnan ya koma jam'iyyar PDP, inda suka ba shi tikitin tsayawa takara kuma ya lashe zaɓen gwamna a lokacin.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki
Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Obaseki, wanda yayi wannan jawabin a Abuja ranar Litinin dangane da sauya sheƙar gwamnoni zuwa APC, yace ba zai shiga wannan layin ba.

Kara karanta wannan

Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno

Sai dai Gwamna Obaseki ya bayyana jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai koma APC a matsayin abin barkwanci.

Yace: "Zamu cigaba da gudanar da mulkin jihar Edo ƙarƙashin jam'iyyar al'umma ta PDP."

PDP zata fara rijista ta yanar gizo

Gwamna Obaseki, wanda shine shugaban kwamitin rijistar zama ɗan jam'iyya, ya bayyana kudirinsa na aiki tuƙuru wajen warware matsalolin jam'iyyarsa ta PDP.

Obaseki, wanda yayi jawabi ga mambobin kwamitin rijista a Abuja, ya roƙi yan Najeriya su cigaba da kasancewa da jam'iyyar PDP domin ceto ƙasar daga halin da APC ta jefa ta.

"Ya kamata yan Najeriya su yi rijista da PDP domin itace jam'iyyar da take ɗauke da hanyoyin warware matsalolin da APC ta jefa su a ciki." inji shi.

A wani labarin kuma Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Nnamdi Kanu

Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta gana da Akanta janar na ƙasa kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: An sanar da ranar fara taron gangamin jam'iyyar APC

Ƙungiyar ta bayyana cewa Nnamdi Kanu ɗan Najeriya ne kuma bai fi ƙarfin doka ba, amma ya kamata a masa adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel