Da Ɗuminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 9
- Yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Kaduna, sun kashe aƙalla mutum 9 a ƙaramar hukumar Zangon Kataf
- Wani mazaunin yankin yace a halin yanzun kowa na cikin tashin hankali, ko gona basa iya zuwa
- Wannan na zuwa kwana uku kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari wani ƙauye daban a cikin wannan ƙaramar hukumar
Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun sake kai hari ƙauyen Makarau Jankasa, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe aƙalla mutum 9, kamar yadda leadership ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Bayan Muƙabala, Rundunar Yan Sanda Ta Gayyaci Sheikh AbdulJabbar Kabara, Ta Faɗi Dalili
Rahoto ya nuna cewa mafi yawan mazauna ƙauyen sun tsere daga gidajensu zuwa ƙauyukan dake maƙwaftaka da su.
Wannan sabon harin na zuwa ne kwanaki uku kacal bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Warkan dake ƙaramar hukuma ɗaya da wannan, inda aka kashe mutum 9 tare da jikkata wasu da dama, kuma aka ƙona gidaje 12, kamar yadda punch ta ruwaito.
Mutanen ƙauyen sun tabbatar da harin
Wani mazaunin ƙauyen, Mr. Donald Bityong, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai ranar Litinin.
Yace yan bindigan sun mamaye ƙauyen Makarau Jankasa ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun kawo ɗauki ƙauyen ne lokacin yan ta'addan sun gama aikin ta'addancin su sun fice.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shehu Sani Ya Caccaki FG Kan Kama Su Nnamdi Kanu, Ya Faɗi Abinda Yafi Muhummanci
Biyonga, yayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su nunka ƙoƙarin da suke yi wajen kare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu.
Yace: "Ba zamu iya jure irin wannan harin ba, domin a halin yanzun babu wanda yake cikin kwanciyar hankali. Babu wanda ya isa yaje gonarsa."
A wani labarin kuma Jega Ya Buƙaci Sanatoci Kada Su Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Ta Naɗin Onochie
Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ya shawarci sanatoci da kada su amince da buƙatar Buhari.
Tshohon shugaban ya shawarci shugaban ƙasa ya maye gurbin Lauretta Onochie, da wata mace a jiharta.
Asali: Legit.ng