ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

  • Hukumar ICPC ta bayyana cewa, idan Najeriya ta dauki matakin karbo kudaden da aka sace, ba za ta sake bukatar bashi ba
  • Kakaklin hukumar ce bayyana haka yayin bikin Tarayya Afrika ta yaki da cin hanci da rashawa da ya gudana a makon nan
  • Hakazalika, ta koka kan yadda ake sanyawa 'yan Afrika sharudda wajen kokarin dawo da kudaden da aka wawure

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce Najeriya ba za ta bukaci bashi daga waje ba idan aka dawo da kudaden da gurbatattun 'yan siyasa da shugabannin kasa suka sata suka kai bankunan kasashen waje.

Kakakin hukumar, Azuka Ogugua, ne ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli a Abuja yayin da take magana a ranar Tarayyar Afirka ta Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ake yi kowacce ranar 11 ga watan Yuli, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Jaridar ta yi ikirarin cewa gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta na fama da kudade kuma ta ci bashin N20.8tn tun lokacin da ta hau karagar mulki a watan Mayun 2015, inda ya kawo bayanai daga Ofishin Kula da Bashi.

KARANTA WANNAN: Yanzu-yanzu: PDP ta je kotu, ta nemi a kwace kujerar gwamna Matawalle da mataimakinsa

ICPC: Da za a dawo da duk kudaden su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi
Janar Sani Abacha | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Datyake magana a matsayin bakuwa a gidan talabijin na Channels, kakakin na ICPC ta ce akwai bukatar a samu manufa daya ta Afirka game da maido da kudaden sata daga Nahiyar ta Afirka.

Ogugua ta ce Matsayin Afirka na gama gari kan dawo da kadara (CAPA) wanda Najeriya ta sanya hannu a kai ya taimaka matuka wajen ganowa da kuma dawo da kudaden da aka wawure zuwa wajen Afirka.

A kalamanta cewa ta yi:

“Lokacin da muke son dawo da kudin, kasashen da ke rike da kudaden suna ba da tsauraran sharudda kamar ma su sake sanya muku haraji. Kudin da aka wawushe daga gare ku, za su ba ku sharadi mai tsauri na kashe kudin, da kuma lura da yadda ake kashe su.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

"Babban misali shi ne yadda Abacha ya wawure kudade, Bankin Duniya ya ba da wani sharadi mai tsauri amma abinda ya fi dacewa dai shi ne, kudadenmu ne."

Ya kamata a dawo da kudaden da aka wawure tare da riba

A karkashin CAPA, kakakin ICPC ta ce kasashen waje da aka tura kudaden da aka wawure su ma yanzu ana ba su wasu sharudda.

Maimakon dawo da asalin darajar kudin, Ogugua ta ce ya kamata kasashen waje su dawo da kudaden tare da riba da suka tara na tsawon shekaru.

Ta ce:

"Lokacin da za ku mayar da kudade, ya kamata ku mayar da su da ainihin darajar yanzu amma ba sa yin hakan. Don haka, suna ba mu sharuddan da za mu bi saboda muna bukatar ba su wasu sharudda, shi ya sa akwai bukatar manufofin Afirka na gama gari."

KARANTA WANNAN: Cikin Hotuna: Wurare 5 masu ban al'ajabi a Najeriya da baku san da labarinsu ba

Kara karanta wannan

Bayan Kammala Mukabala, za a Gurfanar da Abduljabbar Kabara Gaban Kotu

Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi

A wani labarin, Aiki a bankunan kasuwanci a Najeriya ya kasance aiki mai matukar cike takaici, kamar yadda wani matashi mai suna Basit ya koka kan yanayin aikin da yake a banki.

Matashin mai shekaru 28, wanda aka sakaya sunansa don kare bayanansa, yana aiki a matsayin jami'in bayar da kudi a bankin Fidelity a Najeriya tun shekarar 2015.

Shekaru shida, yana reshen Fidelity, yana aiki a matsayin da aka dauke shi, da karamin albashin Naira 68,000 ($ 165) a wata ba tare da karin girma ba.

Ba ka'ida ne aikin Basit ya rasa ba, tsarin da yake aiki a karkashinsa ne matsalar. A rubuce shi ba cikakken ma'aikaci bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.