Cikin Hotuna: Wurare 5 masu ban al'ajabi a Najeriya da baku san da labarinsu ba

Cikin Hotuna: Wurare 5 masu ban al'ajabi a Najeriya da baku san da labarinsu ba

Najeriya kasa ce mai wuraren yawon bude ido da yawa da yawancin mutane a kasar ba su san da shi ba. Wasu wuraren na dauke da dimbin tarihi wani lokacin ma kamar al'mara.

Wadannan wuraren dake jan hankalin 'yan yawon bude ido na da abubuwan al'ajabi dangane dasu kuma Legit.ng ta tattaro muku kadan daga cikin wadannan wuraren.

KARANTA WANNAN: Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani

Legit.ng na gabatar da mahimman wurare 5 NA yawon bude ido a Najeriya:

1. Dutsen Olumo

Dutsen Olumo dake cikin Abeokuta, jihar Ogun. Yayin yakin kabilanci a karni na 19, dutsen ya ba da kariya ga mutanen Egba.

Yana da tsayin mita 137 sama da matakin teku, a cewar Wikipedia.

Dutsen ya zama wurin jan hankalin masu yawon bude ido a shekarar 1976 sannan daga baya shugaban kasa na wancan lokacin, Olusegun Obasanjo ya kaddamar dashi a ranar 3 ga Fabrairu, 2006.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Ga jama'ar Egba, dutsen Olumo bai tsaya kawai a matsayin abin tunawa da imani ba, yana kuma matsayin tushen karfin kasa da kariya da wadatarwa daga Madaukakin Sarki.

VisitNigeriannow yayi rahoton cewa dutsen Olumo yana da kogon karkashin kasa tare da dakuna 5 wadanda suke da fasali daban-daban.

Wuraren shakatawa 5 a Najeriya, da kuma irin abubuwan mamakin dake tattare da baku sani akansu ba
Dutsen Oluma | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

2. Tafkin Sogidi

Tafkin Sogidi dake Awe, wani gari a cikin jihar Oyo. Kifin da ke cikin tabkin an ce suna da kai da hanci irin na mutane.

A cewar wani dan Najeriya mai suna Ojedele Adebayo, wani soja ya rasa 'ya'yansa uku bayan cin kifin da ya kashe a cikin tafkin.

Ya kuma yi ikirarin cewa ana amsa addu'o'i a tafkin.

Wuraren shakatawa 5 a Najeriya, da kuma irin abubuwan mamakin dake tattare da baku sani akansu ba
Tafkin Sogidi | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

3. Kogin Arun

Kogin Arun dake garin Idanre, jihar Ondo, kuma ance yana maganin rashin haihuwa da cututtuka da yawa. Kogin yana cikin wani tuanki ne tsakanin tsaunuka biyu na tsaunukan Idanre.

Kara karanta wannan

Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Wani dan Najeriya da aka ambata da suna Paul ya yi ikirarin cewa wata mata daga jihar Kwara da ke neman haihuwa ta debo ruwa daga Kogin Arun kuma ta haihu bayan ta yi amfani dashi.

Wuraren shakatawa 5 a Najeriya, da kuma irin abubuwan mamakin dake tattare da baku sani akansu ba
Rafin Arun | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

4. Tafkin Iyake

Tafki kadai da aka dakatar a Afirka kuma na biyu a duniya shine ce Tafkin Iyake wanda yake a garin Ado-Awaye a Oke Ogun, jihar Oyo.

Mutanen da na cewa babu wanda ya taba nutsewa zuwa karshen kasan tafkin, tare da yawancin ra'ayoyin da ba a tabbatar da su ba dake cewa zurfin tafkin na kaiwa "zuwa karshen duniya".

A cewar mazauna garin Ado-Awaye, wani farin fata mai bincike ya taba zuwa don gano karshen zurfin tabkin amma bai fito da rai ba.

Wuraren shakatawa 5 a Najeriya, da kuma irin abubuwan mamakin dake tattare da baku sani akansu ba
Tafkin Iyake | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

5. Rafin Al'ajabi

Rafin Al'ajabi yana nan a yankin Nachi a cikin karamar hukumar Udi ta jihar Enugu, kimanin kilomita 4 daga tsohuwar hanyar Kogin Oji/Onitsha.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

A cewar jaridar Vanguard, rafin ya bayyana a cikin al'umma kusan shekaru 42 bayan da ake zargin ya bayyana kuma ya bace a wuri guda.

Wuraren shakatawa 5 a Najeriya, da kuma irin abubuwan mamakin dake tattare da baku sani akansu ba
Rafin Al'ajabi | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Al’ajabi: Rafin da Mutane Masu Neman Haihuwa da Waraka Ke Zuwa Addu’a

A wani labarin daban, An gano wani rafi da mutane masu neman haihuwa da waraka daga cututtuka daban-daban ke zuwa domin addu'a a wani yankin jihar Ondo.

A wata ziyara zuwa tsaunin Idanre da ke a jihar Ondo, tawagar Legit.ng ta gano wani rafi mai ban al'ajabi wanda aka yi ikirarin yana warkar da dukkanin cututtuka, kuma yana magance matsalar rashin haihuwa ga mata.

A cewar Mista Paul, dan jagoran ziyarar, mata da yawa sun bayar da shaida tare da tabbaci na abubuwan al'ajabin rafin inda suka dauki ciki kuma suka haifi yara bayan shan ruwan rafin.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.