Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

  • A jihar Borno, 'yan gudun hijira sun haifi jarirai akalla 17,000 a cikin kasa da shekaru uku a sansaninsu
  • Rahoton kididdiga ya bayyana cewa, an yi kokarin yadda za a samar wa jariran takardun shaidar haihuwa
  • Kungiyoyin tallafawa 'yan gudun hijira na ci gaba da tallafawa jama'ar da aka raba da gidaje a jihar ta Borno

Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce an haifi jarirai 17,053 a sansanonin 'yan gudun hijira na Jihar Borno kakai cikin shekaru uku, BBC Hausa ta ruwaito.

Kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai suna International Organisation for Migration (IOM), ta fada wa kamfanin labarai na NAN cewa an haifi yaran ne a sansani 18 da ke jihar, wadanda kuma aka yi wa rajista daga 2019 zuwa watan Mayun 2021.

Mista Frantz Celestin wanda shi ne shugaban IOM, ya ce sun hada gwiwa da hukumar kidaya ta Najeriya da kuma asusun yara na MDD domin sama wa jariran takardun haihuwa.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

KARANTA WANNAN: Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

Yadda gudun Hijira suka haifi jarirari sama 17,000 a jihar Borno
Dandazon 'yan gudun hijira | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina

Kudurin dokar dake neman haramta bara a kan tituna a jihar Katsina ya zarce karatu na biyu a zauren majakisar jihar a ranar Litinin da ta gabata, Punch ta ruwaito.

Kudurin dokar zartarwa na neman sanya daurin shekara hudu ko zabin biyan tarar N10,000 ga wadanda suka karya dokar a farko, yayin da a karo na biyu za a dawo da mutum asalin jiharsa ko karamar hukumarsa.

Kudirin idan ya zama doka, ya kuma ba da damar korar duk wani mabaracin titi da ba dan Najeriya, zuwa kasarsa.

Kudirin wanda ya samo asali daga Gwamna Aminu Masari, an fara karanta shi a gaban majalisar ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2021 daga Shugaban masu rinjaye, Abubakar Abukur.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

KARANTA WANNAN: Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa

Ya kara da cewa yi musu takardun haihuwa na da matukar muhimmanci sannan kuma yana cikin ayyukansu na tattara bayanai domin bai wa masu bayar da tallafi ga yankin arewa maso gabashin Najeriya.

A cewarsa:

"Mu ne muka fi kowa taimnakawa da matsuguni a Arewa maso Gabas, mafi girma a cikin masu kula da sansanoni, inda muke kula da sansani 115."

KARANTA WANNAN: Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

A wani labarin, Mary Katambi, daya daga cikin ‘yan matan Chibok da ta kubuta daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram a shekarar 2014, ta kammala karatun ta a jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN) da digiri a ilimin lissafi.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya kirkiri jami'ar AUN, ya bayyana a dandalinshi na sada zumunta inda ya watsa hotuna daga bikin wanda aka gabatar a ranar Asabar a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Katambi, wanda ta sanya rigar kammala karatun, ta samu taya murna daga Atiku Abubakar da Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) wanda ya kasance babban mai jawabi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel