Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka sace shugaban wata kwaleji a jihar Zamfara
- 'Yan bindiga sun sace shugaban kwalejin Gona da Kimiyyar Dabbobi a jihar Zamfara da safiyar ranar Lahadi
- An ruwaito cewa, 'yan bindigan sun shiga gidansa ne inda suka sace shi tare da wani mutum a gidan
- Rahotonni sun kuma karin bayani kan cewa, ba a cutar da ko mutum daya daga cikin iyalansa ba
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun sace shugaban kwalejin kimiyyar dabbobin Bakura, Habibu Mainasara, da ke jihar Zamafara a safiyar ranar Lahadi, Channels Tv ta ruwaito.
Wata majiya ta ce, 'yan bindigan sun dauke shi ne da misalin karfe 2:00 na daren yau a gidansa da ke karamar makarantar sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Bakura.
Daya daga cikin ma’aikatan kwalejin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa Mainasara ya koyar a makarantar da aka sace shi.
KARANTA WANNAN: Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida
An yi garkuwa da wani mutum tare da shugaban kwalejin
Majiyar ta ce an yi garkuwa da wani mutum tare da shugaban makarantar, in take cewa:
“Sun shiga gidansa da misalin karfe 2 na dare suka yi awon gaba da shi. Babu wani daga cikin dangin sa da aka taba. Yana zaune ne a gidajen ma'aikata na makarantar sakandaren ko da lokacin da aka nada shi shugaban kwaleji.”
“Ya koyar a makarantar sakandaren tsawon shekaru kuma ya saba da yanayin wurin sosai. Ko da yake kwanan nan ya bayyana damuwa game da tsaron gidansa.
“Hakan ya sa ya yanke shawarar gyara gidansa a hukumance a cikin kwalejin kuma an shirya zai koma gidansa da ke cikin kwalejin a yau amma kafin haka aka sace shi.
“Masu garkuwan sun tuntube mu amma har yanzu ba su nemi kudin fansa ba. Mun roke su kada su azabtar da shi. Sun ce za su yi maganar fansa daga baya."
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, ba a samu jin ta bakinsa ba a lokacin hada wannan rahoton.
KARANTA WANNAN: Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita
Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna
A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun sace mutane shida ciki har da yara a garin Milgoma da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a yayin da 'yan bindigan suka zo da yawa suka afka wa jama'a.
Wani dan acaba da aka kaiwa harin, yanzu haka yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.
Asali: Legit.ng