Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi

Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi

  • Jami'an hukumar NDLEA sun damke tsoho mai shekaru 90 a jihar Katsina kan zargin safarar wiwi
  • Yusuf Yarkadir ya shiga hannun hukumar kan siyar da miyagun kwayoyi ga matasan kauyen na karamar hukumar Rimi
  • Tsohon ya ki sanar da inda yake samun miyagun kwayoyin amma ya ce zai tuba duk da yana ta kokarin haka a baya

Rimi, jihar Katsina

Wani tsoho mai shekaru 90 mai suna Yusuf Yarkadir ga shiga hannun hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan siyar da kwayoyi ga matasa a kauyensu mai suna Yarkadir a karamar hukumar Rimi ta jihar.

Yayin da aka tuhume shi, tsohon ya sanar da cewa shi ke siyarwa matasan yankin wiwi na tsawon shekaru takwas, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: AfDB ta nada Barrow a matsayin sabon shugaban ofishinta na Najeriya

Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi
Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya sanar, duk da wanda ake zargin ya kasa bayyana inda yake samun kayansa, ya sha alwashin barin irin harkar duk da ya so hakan a baya.

Har ila yau, jami'an hukumar NDLEA na jihar Ondo sun damke wasu 'yan uwa biyu tare da sauran wadanda ake zargi da zama dilolin miyagun kwayoyi a babban birnin jihar.

Matasan da aka kama sune: Onyema Sunday mai shekaru 16 da 'yar uwarsa Onyema Amaka mai shekaru 15 an kama su a Car Street dake yankin Akure dauke da 1.9kg na Tramadol a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli.

An kama Kazeem Oluyede mai shekaru 23 a yankin Eru Oba dake babban birnin jihar dauke da 300g na wiwi da 3g na methamphetamine, Daily Trust ta wallafa.

Hakazalika, Maryam Musa mai shekaru 35 ta shiga hannu a yankin Igbara-Oke dake karamar hukumar Ifedore ta jihar dauke da 5.5kg na wiwi duk a rana daya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ba'a ga watan Zhul-Hajji a Saudiyya ba, ranar 20 ga Yuli Sallar Layya

A wani labari na daban, hukumar kula da lamurran 'yan sanda (PSC), a ranar Alhamis ta yi watsi da kudirin karin girma ga tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu.

Hukumar ta ce tana jiran umarni daga ofishin antoni janar na tarayya da ministan shari'a tare da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

Wannan sanarwan na kunshe a wata takarda da aka baiwa manema labarai ta hannun kakakin hukumar, Ikechuckwu Ani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel