Karin Bayani: An Tabbatar da Ɓullar Sabuwar Cutar COVID19 Mai Kisa a Jihar Oyo

Karin Bayani: An Tabbatar da Ɓullar Sabuwar Cutar COVID19 Mai Kisa a Jihar Oyo

  • Gwamnatin jihar Oyo ta tabbatar da ɓullar sabuwar cutar COVID19 mai kisa a jihar
  • Cutar mai suna 'Delta COVID19' ta fara ɓulla ne a ƙasar India, ƙasar da har yanzun take fama da annobar cutar
  • Gwamnatin Oyo ta yi kira ga dukkan matafiyan da suka dawo jihar su keɓe kansu na tsawon kwana 7

An samu ɓullar sabuwar cutar COVID19 mai kisa wadda ake wa laƙabi da 'Delta COVID19' a jihar Oyo, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Anga Wata a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Ranar da Musulmai Zasu Yi Eld-Eil Kabir 1442AH

Taiwo Adisa, mai magana da yawun gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi.

Sabuwar cutar, wanda take da saurin yaɗuwa a tsakanin mutane fiye da ta baya, an fara gano ta ne a ƙasar India.

A jawabinsa, Adisa ya umarci duk wasu matafiya da suka shigo jihar su keɓe kansu na tsawon kwanaki bakwai, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Sabuwar cutar COVID19 ta ɓulla jihar Oyo
Da Ɗuminsa: An Tabbatar da Ɓullar Sabuwar Cutar COVID19 Mai Kisa a Jihar Oyo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace:

"Cutar tana da saurin yaɗuwa, sannan ana kamuwa da ita nan take, saboda haka wannan gargaɗi ne domin tana nan a cikin jama'a."

"Tsarin kowa ya kula da kanshi da gwamnati ta ɓullo da shi za'a cigaba da aiwatar wa, tare da ɗaukar matakan kariƴa kamar takunkumin rufe baki da hanci a inda mutane suke haɗuwa, wanke hannu da dai sauransu."

"Kwamitin yaƙi da COVID19 na jihar Oyo yana kira ga mutanen jihar da su bada haɗin kai wajen yaƙi da wannan cuta ta hanyar yin biyayya ga dukkan matakan kariya."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna

Kowane matafiyi ya keɓe kansa na tsawon kwana 7

Mr. Adisa ya kara da roƙon dukkan wani matafiyi da ya dawo daga ƙasashen waje ya keɓe kansa na tsawon kwana bakwai.

Hakazalika, yace duk wani mazaunin jihar yana da damar samun kulawa ta musamman da kuma yin gwajin cutar kyauta.

A wani labarin kuma Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani

Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, yayi Allah wadai da sace sarkin Kajuru, Adamu Kajuru.

Hon Zailani ya bayyana sarakanunan gargajiya a matsayin ginshiƙan zaman lafiya a tsakanin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel