Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani
- Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, yayi Allah wadai da sace sarkin Kajuru, Adamu Kajuru
- Hon Zailani ya bayyana sarakanunan gargajiya a matsayin ginshiƙan zaman lafiya a tsakanin jama'a
- Ya kuma yi kira ga mutane su kwantar da hankalinsu, yayin da dakarun jami'an tsaro suke ƙoƙarin kuɓutar da su
Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, ya bayyana sace sarkin Kajuru, Alhaji Adamu Kajuru, da wasu yan bindiga suka yi tare da wasu mutum 10 a matsayin abun almara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga
Ya bayyana haka ne a wani jawabi da mai taimaka masa na musamman ta ɓangaren yaɗa labarai, Ibrahim Ɗahiru Ɗanfulani, ya baiwa manema labarai a Kaduna.
Shugaban majalisar dokokin yace labarin sace sarkin Kajuru tare da wasu mutum 10 daga cikin iyalan gidansa abun mamaki ne kuma gwamnati ba zata zauna hakanan ba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Sarakuna na taka muhimmiyar rawa.
Zailani, yace: "Sarakunan gargajiyan mu suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu, saboda haka sace sarkin Kajuru kamar ƙoƙarin wargaza jama'a ne."
Zailani ya ƙara da cewa ko dan muhimmancin sarkin, ya kamata jami'an tsaro su yi gaggawar gano inda yan ta'addan suke kuma su tabbatar sun kuɓutar da dukkan mutanen cikin ƙoshin lafiya.
"Ina kira ga jam'a su kwantar da hankalinsu, muna da tabbacin jami'an tsaro zasu ɗauki matakin da ya dace domin kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya." inji shi.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda
A ranar Lahadi da muke ciki ne, wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka yi awon gaba da sarkin Kajuru tare da wasu mutum 10 daga cikin iyalan gidansa, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu masu garkuwa sun kutsa makarantar sakandiren Bethel Baptist a jihar Kaduna, inda suka sace ɗalibai sama da 120.
A wani labarin haka Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna
Wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun hallaka mutum 9 a wani sabon hari da suka kai Zangon Kataf.
Maharan sun farmaki ƙauyen Warkan, dake ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe ma'aurata da yayansu.
Asali: Legit.ng