Anga Wata a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Ranar da Musulmai Zasu Yi Eld-Eil Kabir 1442AH
- Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli 2021 a matsayin ranar farko a watan Dhul-Hijja
- Sarkin ya bayyana haka ne biyo bayan samun rahotannin ganin wata a wasu sassan Najeriya da ka yi ranar Asabar
- Wannan na nufin musulmai a Najeriya zasu gudanar da sallah babba (Eid-el-Fitr) ranar Talata 10 ga Dhul-Hijja
Sarkin Musulumi kuma shugaban majalisar ƙoli ta addinin musulunci a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli, 2021 a matsayin 1 ga watan Dhul-Hijja 1442AH, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna
Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da shugaban kwamitin harkokikin addinin musulunci na fadar mai martaba sarkin musulmi dake Sokoto, Farfesa Sambo Junaidu, ya fitar ranar Lahadi.
A jawabin nasa, yace:
"Kwamitin dake bada shawarwari kan al'umaran addinin musulunci na fadar sarkin musulmi tare da haɗin guiwar kwamitin duban wata ya samu rahoton ganin jinjirin watan Dhul-Hijja 1442AH."
"Mai alfarma sarkin musulmi ya amince da rahoton kuma ya bayyana Lahadi 11 ga watan Yuli a matsayin ranar farko ta watan Dhul-Hijja 1442AH."
"Sarkin musulmi yana taya ɗaukacin al'ummar musulmin Najeriya murna tare da fatana Allah SWT ya cigaba da tsare su da rahamarsa."
An Jawo Hankalin Musulmi su cigaba da addu'an neman zaman lafiya
Alhaji Sa'ad Abubakar ya kuma roƙi al'ummar musulmi da su cigaba da addu'an neman zaman lafiya da cigaban ƙasa yayin da yake taya su murnan sallah babba dake tafe (Eid-el-kabir), kamar yadda premium times ta ruwaito.
Hukumar dillancin labarai a Najeriya NAN, ta ruwaito cewa watan Dhul-Hijja shine wata na 12 daga cikin jerin watannin addinin musulunci.
Watan yana da matuƙar muhimmanci ga musulman duniya, kasancewa a cikinsa ne mabiya addinin musulunci suke aikin hajji ga waɗanda suka samu iko, kuma suke yin layya.
KARANTA ANAN: Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani
Za'a yi sallah ranar Talata a Najeriya
Saboda bayyana Lahadi 11 ga watan Yuli a matsayin ranar farko a watan Dhul-Hijja 1442AH da sarkin musulmi yayi, al'ummar musulmai zasu gudanar da sallah babba (Eid-el-Kabir) ranar Talata 20 ga watan Yuli.
Ranar tazo dai-dai da 10 ga watan Dhul-Hijja 1442AH, domin a wannan ranar ne ake gudanar da sallah babba.
A wani labarin kuma Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga
Cutar COVID19 ta yi babbar illa ga yan Najeriya yayin da farashin kayan abinci ya ƙaru kuma kuɗin shiga suka ragu
A samu ɓarkewar cutar a karo na farko ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020, kuma ta kashe mutane dama.
Asali: Legit.ng