Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna

  • Wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun hallaka mutum 9 a wani sabon hari da suka kai Zangon Kataf
  • Maharan sun farmaki ƙauyen Warkan, dake ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe ma'aurata da yayansu
  • Wani ɗan yankin yace a halin yanzun mutanen garin sun fara tattara kayan su domin tseratar da rayuwarsu

Wasu yan bindiga sun kashe ma'aurata da ƴaƴansu 3 tare da wasu mutum 4 a wani sabon hari da suka kai ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Warkan dake yankin Gora Gan, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Ƙaduna.

KARANTA ANAN: Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari

Wani mazaunin ƙauyen, Awan Saviour, ya shaida wa jaridar Leadership cewa maharan waɗanda ake zargin fulani ne ɗauke da makamai sun mamaye ƙauyen da misalin ƙarfe 2:00 na daren jiya, inda suka kashe mutum 9 tare da ƙone gidaje 12.

Kara karanta wannan

2023: Rashin tabbas a PDP kan zaben dan takarar shugaban kasa na gaba

A cewarsa maharan sun shiga garin a ƙafa, inda suka buɗe wuta kan me uwa da wabi ga mutanen ƙauyen, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Yan bindiga sun sake Kai hari Kaduna
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Har yanzun babu kwanciyar hankali a ƙauyen yayin da wasu mutane suka fara tattara kayan su domin barin garin sabida ba su san me zaije ya dawo ba."

"Mafi yawancin ƙauyukan dake yankin Kaduna ta kudu suna cikin hatsari, akwai buƙatar jami'an tsaro su kai hari dazukan da muke dasu, domin anan yan ta'addan suke samun mafaka."

Sai bayan harin jami'an tsaro suka kawo ɗauki

Da aka tambaye shi ko jami'an tsaro sun kawo ɗauki ƙauyen yayin da yan ta'addan suka kawo hari, Saviour yace:

"Jami'an tsaro sun ƙariso ƙauyen ne bayan yan ta'addan sun gama aikin ta'addancin su, sun tafi."

KARANTA ANAN: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos

Da aka nemi kakakin yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige, ya bayyana cewa ya fita Kaduna zuwa wani aiki, amma ya alƙawarnta cewa zai nemi cikakken bayani ya sanar a hukumance.

A wani labarin kuma Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Gwamna Zulum na jihar Borno , yace dokar hana fulani makiyaya kiwo a fili ba za ta yi aiki ba.

Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel