Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda
- Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-hare da aka kai kwanan nan jihar Zamfara da Kaduna
- Shugaban ya umarci sojoji da su ɗauki matakin murkushe duk wasu yan ta'adda ta yaren da zasu fahimta
- Buhari yayi kira ga yan siyasa da su zo a haɗa hannu wajen lalubo hanyar samun nasara, ba wai su yi ta magana ba
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya buƙaci sojoji su ɗauki matakin murƙushe yan ta'adda baki ɗaya, biyo bayan hare-haren rashin imani da aka kai jihohin Zamfara da Kaduna.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna
Shugaba Buhari, wanda yayi Allah wadai da hare-haren da aka kai jihohin biyu, ya umarci sojojin Najeriya da su ɗauki mataki kan wannan yanayin mara daɗi ta yaren da zasu fahimta.
Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta facebook.
Shugaban ƙasa ya ƙara da jaddada umarnin sa cewa sojoji su ɗauki matakin murkushe yan ta'addan dake kashe yan Najeriyan da basu ji ba ba su gani ba a yankunan karkara.
Buhari, yace: "Sojoji da sauran hukumomin tsaro suna aiki da sabbin dabaru da tsare-tsare wanda yake haifar da ɗa mai ido a wasu daga cikin jihohin da lamarin yafi ƙamari."
"Muna kira garesu da su ɗauki matakin murƙushe yan ta'adda baki ɗaya, waɗanda suke kashe yan ƙasa da ba su ji ba kuma ba su gani ba a yankunan karkara."
Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa da maganganun yan siyasa
Shugaba Buhari yayi Allah wadai da wasu maganganun yan siyasa game da tsaron ƙasa, ya roƙe su da su zo a haɗa hannu da su wajen lalubo hanyoyin warware ƙalubalen dake fusakantar Najeriya.
Ya kuma bayyana halin baƙin ciki da ƙasar ta shiga saboda yawaitan rasa rayuka, inada ya roƙi jami'an tsaro su yi duk me yuwu wa domin kare faruwar hakan nan gaba.
KARANTA ANAN: Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari
Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya dangane da wannan labarin.
Musa D. Mustapha, yace:
"Abun takaici ne yadda ake rasa rayuka a jihohin Zamfara, Katsina, da Neja, manoma ba su samun damar zuwa gonakin su yayin da muke cikin lokacin damuna."
"Yin Allah wadai da ayyukan waɗannan mutanen daga Abuja bai isa ba, waɗannan mutanen ansan inda suke, meyasa gwamnati ba zata ɗauki tsattsauran mataki akan su ba?"
Ahmed Zakaria, yace:
"Ba da jimawa ba yan ta'adda zasu gane abinda ake nufi da yaren da zasu fahimta. Ina gargaɗin ku, idan kuna ganin ba wata barazata bace, to zaku shaida da idanunku."
Abubakar Buba Vana, yace:
"Dan Allah muna bukatar ɗaukar mataki ne a aikace ba wai a baki ba, aiki shine gaba da yin magana."
Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa
A wani labarin kuma Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu
Hukumar makarantar Bethel Baptist ta ce ta kaiwa yan bindiga buhun shinkafa 9 amma sun ƙi amsa.
Yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar a Kaduna sun nemi iyaye da hukumar makarantar su bada abinci.
Asali: Legit.ng