Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci da Ƙarancin Kuɗin Shiga

Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci da Ƙarancin Kuɗin Shiga

  • Cutar COVID19 ta yi babbar illa ga yan Najeriya yayin da farashin kayan abinci ya ƙaru kuma kuɗin shiga suka ragu
  • A samu ɓarkewar cutar a karo na farko ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020, kuma ta kashe mutane dama
  • Wasu farashin na kayan abinci a kasuwanni sai da suka nunka biyu ko sama da haka saboda kulle

Wani ɗan Najeriya, Opeyemi Adeyemi, yana aiki a ɗaya daga cikin manyan kamfanonin kuɗi a Najeriya, an rage masa albashinsa lokacin kulle saboda annobar COVID19.

Ya bayyana cewa ya zama wajibi ka amince da rage albashi idan kana son cigaba da aiki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda

Adeyemi, ɗan kimanin shekara 42, kuma kwararre a ɓagaren kuɗi, wanda yake zaune a Obalende, jihar Lagos, yace:

"Farashin kayan abinci ya wuce tunani na, na kan zauna da matata mu tattauna akan lamarin, yayin da take shayar da ɗan mu na biyu, domin ya zama wajibi mu canza abincin dare, mu koma cin gari ko taliyar yara maimakon dafa abinci sau uku a rana."

Kara karanta wannan

Wani babban Jigon PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

"Farashin ya yi mun yawa da iyalai na waɗanda suke ƙarƙashi na. An zabtare mun albashi da kashi 30%, ga shi na kashe duk wata ajiyata wajen ɗaukar nauyin iyalai na."

"Hakanan kuɗin da muke biya na wutar lantarki ya ƙaru, kuma duk da haka wani lokacin dole na siyo man fetur domin tayar da injin wuta."

Farashin kayan Abinci
COVID19: Magidanta a Najeriya Na Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Adeyemi na ɗaya daga cikin miliyoyin yan Najeriya da suka fuskanci ƙarancin kuɗin shiga saboda rasa aikin su ko kuma rage musu albashin su, musamman lokacin kulle na annobar korona virus.

Wannan binciken zai bayyana yadda sakamakon ɓarkewar annobar COVID19 ta shafi farashin abinci a Najeriya, kasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar Africa.

Abunda yan Najeriya suka fuskan lokacin COVID19

A ranar 27 ga watan Fabrairu, aka gano wanda ya kamu da cutar na farko a ƙasar, tun daga wannan lokacin cutar ta yaɗu a sauran sassan ƙasar kuma aka rasa rayuka.

Kara karanta wannan

Da Tunanin Yan Najeriya a Zuciya Shugaba Buhari Yake Bacci, Gwamna

Dokar zaman gida da aka saka ya illata dukkan hanyoyin tattalin atziƙi a ƙasar, da duniya baki ɗaya, yayin da wasu ƙasashen suka rinƙa bullo da dabaru domin daƙile lamarin.

Lokacin da cutar ta yaɗu sosai a 2020 sai da ta canza tafiyar tattalin arziƙin ƙasar, ta shafi rayuwar jama'a tare da iyalai da dama da ɗai-ɗaikun mutane waɗanda suka yi ta fama da baƙon yanayin da suka tsinci kan su a ciki.

Farashin kayan abinci ya nunka a ƙasuwanni

A bayanan binciken da aka gudanar kwanan nan na farashin abinci a kasuwanni ya nuna cewa yan Najeriya sun samu ƙarin kashi 66.8% na farshin kayan masarufi daga watan Fabrairu, 2020, lokacin da cutar ta shigo, zuwa watan Maris 2021, lokacin da aka gudanar da binciken.

Binciken farashin kayan abinci
COVID19: Magidanta a Najeriya Na Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Binciken wanda aka gudanar a jihohi 13 ya nuna cewa yanayin farashin kayan abinci ya haɗu da kuɗin da yan Najeriya suke biya na wuyar lantarki.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

Jihohin da aka gudanar da binciken sun haɗa da, Anambra, Benuwai, Enugu, Ebonyi, Birnin tarayya Abuja, Kano, Kwara, Lagos, Neja, Ogun, Ondo, Oyo, da kuma Sokoto.

Binciken ya taɓo mafi yawan kayan abincin da aka fi amfani da su a gidajen yan Najeriya kamar, shinkafa, wake, gari, Mai, kifi, doya, tumaturi, albasa, gyaɗa, burodi da dai sauransu.

Saboda yawaitar hare-hare da rashin zaman lafiya a wasu jihohin yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma, yasa aka dakatar da binciken a iyakar jihohin dake da zaman lafiya.

KARANTA ANAN: Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Taswirar jihohin da ka gudanar da bincike
COVID19: Magidanta a Najeriya Na Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Adadin ya za'a alaƙanta hauhawar farashin abinci da COVID19?

Binciken da aka gudanar kan ra'ayoyin magidanta dake siyen kayan abinci kamar Adeyemi, ya nuna cewa annobar korona da wasu abubuwa da suka shafe ta suke da alhakin kashi 69% na ƙaruwar farashin kayan abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata

Kamar yadda sauran ƙasashen duniya suka ɗauki mataki, gwamnatin Najeriya ta ɗauki babban matakin kare yaɗuwar cutar, inda a ƙarshen watan Maris 2020, gwamnati ta dakatar da komai.

Wannan matakin ya tsayar da ayyukar samar da kayan amfani, tafiye-tafiye, da duk wasu al'amuran tattalin arziƙi.

Rashin tsaro da kulle iyakoki ya taka muhimmiyar rawa

Yayin gudanar da wannan binciken, an zanta da wasu yan Najeriya kan a ganin su waɗanne abubuwa ne suka jawo ƙaruwar farashin kayan abinci.

Manufar yin hakan shine a fahimci sauran abubuwan da yan Najeriya suke ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙarin farashi a kayan abinci.

Daga cikin ra'ayoyin yan Najeriya 2,351 da aka tattauna da su, mutum 1,610 (69%) sun bayyana cewa ƙarancin kayan abincin da kuma ƙaruwar neman su lokacin dokar kulle shine ya jawo yawan hauhawar farashin.

Hakazalika, matsalar tsaro da rashin zaman lafiya musamman a yankin arewa maso gabas ya taka rawa wajen ƙarancin kayan abinci da kuma rashin samar da su a yankin.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda

Sauran abubuwan da yan Najeriya ke ganin ya jawo wannan lamarin sune rufe iyakoki da gwamnati ta yi da kashi 3%, sai kuma satar mutane, aikin yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya, suma sun taka rawa da kashi 4%

Lamarin yafi shafar iyaye mata

Morufat Oluyemi, dake aikin gyaran gashi a Arepo, jihar Ogun, tace dole ta sa take aiki kala biyu kullum domin ta samu kuɗinda zata kula da yaranta 4 bayan mijinta ya mutu.

Tace: "Dole nake aiki kala biyu, inada shagon gyaran gashi, amma abinda nake samu ba zai isheni na ɗauki nauyin iyalina ba. Hakan yasa. nake aikin shara domin ƙara samun kuɗin shiga."

"Gari na ɗaya daga cikin abinda muka fi amfani da shi, amma tunda farashin kayan abinci ya ƙaru, abun ya zama da wahala ga 'yayana. Ina fatan wannan wahalar zata ƙare ba da jimawa ba. Yanzun bani da isasshen lokaci da zan baiwa yara na saboda aiki."

Kara karanta wannan

Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

Me gwamnati ta yi na ɗaukar mataki kan lamarin

Gwamnatin Najeriya a matakin tarayya ta yi namijin ƙoƙari wajen samar da wasu kayan abinci ga yan Najeriya, musamman talakawa na can ƙasa.

Duk da ƙoƙarin gwamnati na raba kayan abinci ga yan Najeriya aƙalla 10 miliyan, amma sai da cin hanci da rashawa ya shiga cikin tsarin.

Kuma hakan ya sa mutane suka ɓalle wuraren ajiye kayan abinci, suka ɗiba son ransu lokacin zanga-zangar #EndSARS.

Amma gwamnatin Najeriya bata shiga lamarin yawan hauhawar farashin kayan abinci ba, da zummar dakatar da lamarin.

A wani labarin kuma Da Tunanin Yan Najeriya a Zuciya Shugaba Buhari Yake Bacci, Gwamna

Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya yaba da ƙoƙarin da shugaba Buhari yake na kawo cigaba a Najeriya.

Badaru yace shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma da tunanin yan Najeriya yake bacci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel