Da Tunanin Yan Najeriya a Zuciya Shugaba Buhari Yake Bacci, Gwamna
- Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya yaba da ƙoƙarin da shugaba Buhari yake na kawo cigaba a Najeriya
- Badaru yace shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma da tunanin yan Najeriya yake bacci
- Shugaban APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni, ya taya sanata Bent murnar shigowa jam'iyya mai mulki
Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, ya bayyana cewa shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da riƙon amana kuma "Yana kwanciya bacci da yan Najeriya a zuciyarsa," kamar yadda the cable ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata a Nasarawa
Yace shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi abubuwa da dama ga yan Najeriya ta ɓangaren kyautata rayuwarsu da kuma cigaban tattalin arziƙi da walwala, kamar yadda punch ta ruwaito.
Gwamnan ya kuma yaba wa Buhari bisa tsare-tsaren da ya ƙirƙiro wajen haɓɓaka tattalin arziƙi, musamman tsarin NSIP na gyara ɓangaren noma a ƙasar nan.
Gwamnan yayi wannan jawabai ne a wurin taron ƙarbar Graxe Bent, tsohon sanata mai wakiltar Adamawa ta kudu, wanda ya fice daga PDP zuwa APC ranar Asabar a Yola.
Yace: "Buhari mutum ne mai gaskiya da riƙon amana, kuma a kullum da tunanin yan Najeriya yake kwanciya bacci."
"Yanzun yan Najeriya sun fara ganin namijin ƙoƙarin da shugaba Buhari yake yi, shiyasa suke sauya sheƙa zuwa APC."
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda
Shugaban APC ya yaba da matakin Bent
Shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya taya sanata Bent murnar shigowa jam'iyya mai mulki.
Buni, wanda tsohon shugaban majalisar dattijai ta kasa, Ken Nnamani, ya wakilta, yace za'a dama da Sanata Bent kamar yadda ake yiwa kowane mamban APC.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna
Wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun hallaka mutum 9 a wani sabon hari da suka kai Zangon Kataf.
Maharan sun farmaki ƙauyen Warkan, dake ƙaramar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna, inda suka kashe ma'aurata da yayansu.
Asali: Legit.ng