Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata a Nasarawa

Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata a Nasarawa

  • Wasu yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da miji da mata a jihar Nasarawa
  • Rahoto ya nuna cewa waɗanda aka sace ɗin ma'aikatan gwamnatin ƙaramar hukumar Toto ne dake Nasarawa
  • Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Mr Gabriel Hagai, ya tabbatar da aukuwar lamarin

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da, Yohana Isheme, da matarsa, Naomi Yahana a garin Ukya Sabo, ƙaramar hukumar Toto, jihar Nasarawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda

Wani mazaunin garin Ukya Sabo mai suna, Samuel, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

Yace ɓarayin sun mamaye ƙauyen da daddare ɗauke da manyan makamai, da isar su kowa ya ɗauki matsaya cikin dabaru kafin daga bisa ni wasu su kutsa cikin gidan.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

Yan bindiga sun sace mata da miji a Nasarawa
Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata a Nasarawa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "Yan bindigan sun ɓalla ƙofar baya, inda suka tafi kai tsaye zuwa ɗakin kwanan abun harin su, inda suka tafi da shi tare da mai ɗakinsa."

Ya ƙara da cewa maharan sun yi ta harbin iska domin tsoratar da maƙotan mutumin yayin da suka fito da shi.

Waɗanda aka sace ma'aikatan gwamnati ne

Rahoto ya nuna cewa Isheme, ma'aikaci ne a sashin lafiya na ƙaramar hukumar Toto, yayin da matarsa kuma malama ce a makarantar Firamare dake Tika.

Kakakin ƙaramar hukumar Toto, Mr Gabriel Hagai, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Kashe Mata da Miji, 'Yayansu 3 da Wasu Mutane da Dama a Sabon Hari a Ƙaduna

Amma kakakin hukumar yan sanda na jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, yace har yanzun bai samu rahoton aukuwar lamarin ba.

"Zan tuntuɓi DPO dake kula da ƙaramar hukumar domin tabbatar wa a hukumance, sannan in sanar."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

A wani labarin kuma Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sha alwashin hukunta duk wani ɗan ta'adda.

Buhari ya nuna alhininsa bisa mummunan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262